Lamari ya yi zafi: Dole mu nemo tsoffin sojoji don a yaki ta'addanci, inji CDS

Lamari ya yi zafi: Dole mu nemo tsoffin sojoji don a yaki ta'addanci, inji CDS

  • Babban hafsan tsaron Najeriya ya bayyana bukatar a dama da tsoffin sojoji wajen magance rashin tsaro
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wasu tsoffin sojoji a jihar Adamawa jiya Talata
  • Ya bayyana cewa, idan tsoffin sojoji suka ba da hadin kai ne za a iya samun dabaru wajen magance matsalar

Adamawa - Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor, ya ce Sojojin Najeriya za su nemo jami’an sojojin da suka yi ritaya don magance matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso gabas.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata 24 ga watan Agusta a wani zaman tattaunawa na kwana daya tare da manyan jami’an da suka yi ritaya daga shiyyar arewa maso gabas da aka gudanar a runduna ta 23 da ke Yola, jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Lamari ya yi zafi: Dole mu nemo tsoffin sojoji a yaki ta'addanci, in ji CDS
CDS Lucky Irabor | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

A jawaban da ya gabatar, Irabor ya ce:

“Yana daga cikin dalilin da ya sa nake nan tare da tawaga ta, don damawa da manyan abokan aikinmu da suka yi ritaya domin neman cikakkiyar mafita game da yadda za a kawo karshen rashin tsaro a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun yi imanin cewa yayin da muke damawa da su, za su kasance a shirye don bude mana hanya a wuraren da za su inganta tsaro, kuma za su iya gaya mana wuraren da kuskuren mu ne don mu yi gyara."

Tsaron Arewa maso gabas na hannun 'yan yankin

Ya jaddada cewa mafita ga kalubalen tsaro a arewa maso gabas yana hannun mutanen arewa maso gabas.

A cewarsa:

"Mun yi imanin cewa, musamman, maganin matsalar tsaron arewa maso gabas zai dogara ne kacokan kan gudunmowowin da suka fito daga yankin.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

A rahoton Nigerian Tribune, ya kuma ba 'yan Najeriya tabbacin cewa, lamarin rashin tsaro zai kau, kuma tsaron kasar zai inganta nan ba da dadewa ba.

Ya ce:

"Hakanan, mun yi imanin cewa a cikin kwanaki masu zuwa, tsaro zai inganta kuma ya yi kyau a yankin da Najeriya baki daya."

Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin 'yan bindiga

A wani labarin, 'Yan majalisar dokokin jihar Katsina biyu, a ranar Litinin, sun fashe da kuka a bayyane bisa yawan hare-haren da aka kai kwanan nan a cikin al'ummomin jihar ta Katsina, The Cable ta ruwaito.

Da yake magana ranar Litinin a zauren majalisar wanda kakakin majalisar Tasi’u Maigari ke jagoranta, Shehu Dalhatu-Tafoki, mataimakin kakakin majalisar, ya gabatar da wani kudiri na “mahimmantar da bukatar jama’a cikin gaggawa” kan matakin rashin tsaro a jihar.

A cewar Dalhatu-Tafoki, mamba mai wakiltar mazabar Faskari, duk da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi, da hukumomin tsaro, har yanzu al’ummomi na fuskantar hare-hare.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel