Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

'Yan Najeriya sun yi mamaki da jin labarin cewa 'yan bindiga sun kai hari a Makarantar sojoji ta Najeriya (NDA), wacce ake ganin tana daya daga cikin wurare mafi aminci a kasar, a ranar Talata, 24 ga watan Agusta.

'Yan bindigar sun kashe sojoji biyu tare da yin garkuwa da wani jami'i yayin harin, a cewar PR Nigeria.

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara
NDA ya kasance makarantar horar da sojoji na Najeriya Hoto: Nigerian Defence

Yayin da sojoji suka fara bin sawun ‘yan bindigar da ba a sani ba da nufin bin diddigin maharan da kubutar da jami’in da aka sace, Legit.ng ta tattara wasu dalilan da ka iya zama wadanda suka sa aka samu tabarbarewar tsaro a makarantar.

1. Tangarda a cikin babban tsarin tsaro na NDA

Wani babban dalilin da ya sa 'yan fashin suka samu nasarar yin kutse a tsarin tsaron makarantar shi ne saboda tangarta a tsaron.

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Mai magana da yawun NDA, Manjo Janar Benjamin Sawyer, ya shaida wa PR Nigeria cewa 'yan fashin sun kutsa cikin babban harabar NDA sannan suka tafi kai tsaye zuwa kwatas din jami’ai.

Wannan bayanin yana nuna cewa maharan na iya satar shiga cikin harabar cibiyar soji ba tare da an gano su ba.

2. 'Yan bindigar sun san inda wadanda suke hari suke

Wata hujjar da ta ba wa 'yan fashin damar samun nasarar kai farmaki a makarantar ita ce, saboda wataƙila sun gudanar da bincikensu na sirri game da makarantar don sanin inda kwatas din jami'an suke kafin su kai hari.

Wannan a bayyane yake tunda maharan sun tafi kai tsaye zuwa sashin jami'an bayan yin kutse a tsarin tsaron da nufin yin garkuwa da manyan hafsoshi don neman kudin fansa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

3. Har yanzu FG na ci gaba da raina kayan yaƙi na ‘yan bindigar

Dalili na uku da ya sa farmakin da aka kai wa NDA ya faru shi ne cewa gwamnatin tarayya da hedkwatar tsaro suna yin kuskure na raina ƙarfin ‘ya ta’addan kamar yadda aka raina Boko Haram lokacin da suka fara.

Ga dukkan alamu gwamnatin Najeriya tana wasa da wuta duba da yadda yan fashin suka san cewa suna da manyan makamai don kai farmaki kan NDA inda jami'an soji ke samun horo.

Kasancewar barayin a cikin watan Yuli sun harbo wani jirgin yaki na sojan sama yana tabbatar da cewa wadannan 'yan bindigar suna da isassun makamai don yakar sojojin Najeriya.

NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

A baya mun kawo cewa makarantar horar da Sojin Najeriya (NDA) ta tabbatar da kisan jami’ai biyu a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari barikin a ranar Talata, 24 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na makarantar, Manjo Bashir Jajira ya fitar, ya ce 'yan bindigar sun sace wani jami'i, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

NDA ta bayyana cewa tana kan bin diddigin 'yan fashin da suka yi kutse a tsarin tsaronta, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel