Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

  • Shugaban majalisar dattawa a Najeriya ya bayyana shakkunsa game da 'yan ta'adda masu mika wuya
  • Shugaban ya ce, watakila a samu wasu wadanda suke tuban muzuru daga cikin 'yan ta'addan
  • Ya kuma bayyana bukatar a samar da tsarin da zai ke tantance masu tuban gaskiya da na karya

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce dole ne ‘yan Najeriya su yi taka tsantsan wajen karbar 'yan Boko Haram da ke ikirarin sun mika wuya kuma suna neman gafara, in ji rahoton The Cable.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Litinin 23 ga watan Agusta, Lawan ya ce dole ne a samar da matakan da za su tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun yi tuban gaskiya.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa ba zamu iya kashe yan Boko Haram da suka mika wuya ba, Lai Mohammed

Hedkwatar Tsaro (DHQ) ta ce sama da 'yan ta'adda 1,000, ciki har da kwamandojin Boko Haram da kwararrun sarrafa bama-bamai sun mika wuya ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya.

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan
Tubabbun 'Yan Boko Haram | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mutane da yawa sun yi Allah wadai da matakin gwamnatin tarayya na yafiya, gyara da sake shigar da tubabbun 'yan ta'addan cikin al'umma.

Shugaban majalisar dattawa ya ce kasar na bukatar manufa mai tasiri kan yadda za a tunkari masu aikata laifuka da suka tuba.

A cewarsa:

"Muna bukatar tantance wadanda suka yi tuban gaskiya da wadanda suka mika wuya kawai saboda wasu dalilai, amma ba wai ina da ra'ayin cewa a manta da mutanen da ke mika wuya ba, dukkan su 'yan ta'adda ne da sauran su."

Lawan ya kuma bayyana yafiya da karbar tuban 'yan ta'adda yana daya daga cikin dokokin yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Da yake bayyana shakkunsa da kuma neman a samar da tsari wajen karbar tubabben 'yan ta'adda, Lawan ya ce:

"Na yi imanin cewa ya kamata mu kawar wa mutane shakku, amma kuma ya kamata mu yi taka tsantsan kan wadanda watakila ba da gaske suke ba, duk da ya kamata mu karbi mutane lokacin da suka zo suka dauki matakan da suka dace, amma a samu dabarun da suka dace akan yadda za a magance sake shigar da irin wadannan mutane cikin al’umma.”

Lawan ya ce yanayin tsaro a kasar zai inganta kafin shugaba Buhari ya sauka a 2023.

Ya kara da cewa:

"Kafin wannan gwamnatin ta fita da yardar Allah a 2023, lamarin tsaro zai inganta, fiye da yadda yake a yau."

Shugaban na majalisar dokoki ya kara da cewa majalisar kasa tana aiki don tabbatar da cewa an samar da isassun kudade ga hukumomin tsaro a cikin kasafin kudin 2022.

Kara karanta wannan

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

A wani rahoton na daban, shugabannin gargajiya da na addini a Borno sun ce zai yi wahala a sake karbar 'yan Boko Haram da suka tuba cikin garuruwa su.

Shugabannin sun bayyana fargaba kan yadda sojojin Najeriya za su raba tubabbun 'yan Boko Haram da tsattsauran ra'ayi a karkashin shirin su na Safe Corridor, jaridar The Cable ta ruwaito.

Abubakar El-Kanemi, Shehun Borno, ya ce wannan abu ne mai kyau, amma mutane za su ci gaba da kasancewa cikin fargaba na bala'in tashin hankalin da aka shafe shekaru 12 ana yi, musamman mazauna garuruwan da za a mayar da masu tayar da kayar bayan.

Karin 'yan Boko Haram sun mika kansu ga sojoji, suna rokon gafaran 'yan Najeriya

A wani labarin, Rahoto daga Daily Trust na shaida cewa, wasu mayakan Boko Haram sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

A cewar majiyoyin soji, ‘yan ta’adda 190 sun mika wuya a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a ranar Asabar.

An tattaro cewa mazauna garin sun yi mamaki lokacin da suka ga dimbin 'yan ta'addan da suka isa garin Mafa a ranar Asabar.

A cewar majiyar tsaro, wadanda suka mika wuya sun hada da manyan mayaka, sojojin kafa, matansu da yaransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.