Dakarun Sojoji Sun Fafata da Yan Bindiga Sun Kubutar da Matafiya a Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Fafata da Yan Bindiga Sun Kubutar da Matafiya a Kaduna

  • Sojojin Operation Safe Haven sun kuɓutar da wasu matafiya 15 daga hannun yan bindiga a jihar Kaduna
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka
  • Yace dakarun sun kai ɗauki garin Jagindi, karamar hukumar Jema'a bayan an sanar da su abinda ke wakana

Kaduna - Dakarun sojin Operation Safe Haven sun kubutar da wasu matafiya 15 da yan bindiga suka sace a Jagindi, karamar hukumar Jema'a, jihar Kaduna ranar Lahadi, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Yace sojojin sun kai ɗauki ne bayan wani kiran gaggawa da aka musu ƙan lamarin sace matafiyan.

Sojoji sun kubutar da matafiya a Kaduna
Dakarun Sojoji Sun Fafata da Yan Bindiga Sun Kubutar da Matafiya a Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sojoji sun dakile harin yan bindiga

Aruwan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dakarun sojin sun kai ɗauki inda suka fatattaki yan bindigan tare da kubutar da matafiya 15."
"Maharan sun yi awon gaba da matafiya su 15 ne daga motoci biyu a yankin yayin da suke tsaka da tafiya."

Kwamishinan ya bayyana sunayen mutanen da sojojin suka kuɓutar, da suka haɗa da, Maisaje Pam, Samuel Peter, Ziyau Abdul, Henry Dabo, Abduljabar Auwal, da Muhammad Ali.

Sauran sune; Dama Dabo, Ramatu Aminu, Muhammad Sani, Abdullahi Muhammad, Bashar Garba, Abubakar Musa, Saad Yakubu, Maryam Ibrahim, da kuma Lami Bitrus, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnatin Kaduna ta yaba da kwazon sojoji

A cewar Mista Aruwan, mukaddashin gwamnan jihar, kuma mataimakiyar gwamna, Hadiza Balarabe, ta jinjina wa sojojin bisa kai ɗauki cikin gaggawa.

Sojojin na cigaba da gudanar da Operation din bincike da kuma kubutar da mutane a yankin.

Duk da kokarin da jami'an tsaro suke na magance matsalar tsaron jihar Kaduna, yan bindiga na cigaba da cin karen su babu babbaka wajen watsa mutanen kauyuka, suna kashe wasu sannan su sace wasu.

Wasu na samun sa'ar kubuta daga hannun ɓarayin bayan an biya kuɗin fansa, wasu kuma suna cigaba da tsare su a daji na tsawon makwanni da watanni.

A wani labarin kuma Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Wanda Ya Dace Ya Gaji Shugaba Buhari a 2023

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace duba da halin da Najeriya ke ciki tana bukatar shugaba ɗan zamani.

Gwamnan yace ya zama wajibi yan Najeriya su yi wa kansu karatun ta natsu wajen zaɓen shugaba a 2023, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel