Sojojin hadaka sun ragargaji 'yan Boko Haram da ISWAP a Borno, sun hallaka wasu adadi

Sojojin hadaka sun ragargaji 'yan Boko Haram da ISWAP a Borno, sun hallaka wasu adadi

  • Rundunar sojin hadaka ta MNJTF sun hallaka wasu adadi na 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP
  • Sun kuma raunata da dama, yayin da wasu da yawa suka gudu da raunukan harbin bindiga
  • Rahoto ya bayyana cewa, soja daya ne ya ji rauni kuma tuni an mika shi ga asibiti domin masa jinya

Borno - Sojojin runduna ta hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) da ke jibge a yankin tafkin Chadi sun kashe mambobin kungiyar Boko Haram da ISWAP, The Cable ta ruwaito.

Muhammad Dole, jami’in yada labarai na MNJTF ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce sojojin na Sashi na 3 sun yi nasarar dakile wani kwanton bauna da 'yan ta'addan suka yi yayin da suke sintiri na yau da kullum a kan hanyar Gajiram zuwa Monguno na jihar Borno.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

Dole ya ce an hallaka maharan guda hudu yayin da da yawa suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Sojojin hadaka sun ragargaji 'yan Boko Haram da ISWAP a Borno, sun hallaka wasu adadi
Sojojin Hadaka | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa soja daya da ya samu rauni a harin yana jinya a wani asibiti na sojoji.

A cewarsa:

“Abubuwan da aka kwato sun hada da: bindigogin AK47 guda uku, harsasai guda 10 (7.62mm) na musamman, 3HG guda daya, madaukin magazine guda daya, magunguna iri iri da abin tsefe gashi daya da dai sauran abubuwa."

“A lokacin ziyarar sa na aiki na kwanan nan zuwa matakan sassa, Kwamandan Rundunar MNJTF, Maj.-Gen. Abdul-Khalifah Ibrahim, ya umarci sojojin da su kara kaimi kuma su dauki matakin nuna karfin hali wajen tunkarar masu tayar da kayar baya don hana su sakat.
"FC din ya yabawa sojojin tare da sake jaddada kudurin sa na farko na bayar da tallafin da ya dace don murkushe sauran masu aikata laifuka a duk fadin yankin."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

Gidan Soja: Dalilin da yasa muke karbar tuban mayakan Boko Haram da suka mika wuya

A bangare guda na batun yafewa 'yan Boko Haram, rahotanni sun bayyana cewa Sojojin Najeriya sun yi bayanin cewa babbar yarjejeniya ta duniya wanda Najeriya ta sanya hannu a kansa bai yarda a kashe 'yan ta'adda da suka mika wuya ba.

Leadership ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Brig-Gen Onyema Nwachukwu ne, ya bayyana haka a wata hira.

Ya sake nanata cewa sojojin da aka tura don “Operation Hadin Kai” sun karbi ‘yan ta’addan Boko Haram/ ISWAP da suka mika wuya bisa ga dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar rikicin makamai.

Karin 'yan Boko Haram sun mika kansu ga sojoji, suna rokon gafaran 'yan Najeriya

A wani labarin daban, Rahoto daga Daily Trust na shaida cewa, wasu mayakan Boko Haram sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.

A cewar majiyoyin soji, ‘yan ta’adda 190 sun mika wuya a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a ranar Asabar. An tattaro cewa mazauna garin sun yi mamaki lokacin da suka ga dimbin 'yan ta'addan da suka isa garin Mafa a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

A cewar majiyar tsaro, wadanda suka mika wuya sun hada da manyan mayaka, sojojin kafa, matansu da yaransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: