An hallaka makiyaya 3 a wani sabon harin ramuwar gayyar 'yan bindiga a Kaduna

An hallaka makiyaya 3 a wani sabon harin ramuwar gayyar 'yan bindiga a Kaduna

  • Daga jihar Kaduna, an hallaka wasu makiyaya a wani harin ramuwar gayya da aka kai wani kauye
  • Rahoto ya bayyana cewa, akalla mutane uku ne suka mutu, sannan wasu da dama sun jikkata
  • Rahoton ya fito ne daga ofishin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwa

Kaduna - Rahotanni sun ce an kashe wasu makiyaya uku a wani harin ramuwar gayya da wasu ‘yan bindiga suka kai wa Ribok, Tsoriyang da Kankada da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi 22 ga watan Agusta, Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya ce harin na ramuwar gayya ne a kauyen Ungwan Dooh na karamar hukumar, The Cable ta ruwaito.

Ya ce 'yan bindigar sun nufi harin ga gidan wani mutum ne Ardo Tanko Usman, inda mutane uku da ke cikin gidan aka hallaka su.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutum 14 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Sake Kai Hari Jihar Kaduna

An hallaka makiyaya 3 a wani sabon harin ramuwar gayyar 'yan bindiga a Kaduna
'Yan bindiga | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: Twitter

Wadanda aka kashe din sun hada da Bayero Wake, Isah Usman da Abu Usman.

A sanarwar, Aruwan ya ce:

“Mazauna hudu sun ji rauni. Su ne Ambo Jamo, Sule Ambo, Muazu Ori da Ibrahim Mohammed."
“An kone tare da lalata mota daya, gidaje uku da bukkokin makiyaya takwas. Sojoji da 'yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru tare da kwashe makiyaya da yawa domin kare lafiyarsu.
“Ana ci gaba da ayyukan bincike da ceto kuma za a ba mazauna labarin duk wani ci gaba da aka samu.
“Mukaddashiyar gwamna Dr Hadiza Balarabe ta karbi rahoton cikin bacin rai tare da yin tir da yadda ake kashe-kashe da ramuwar gayya a yankin.
"Ta yi addu'ar Allah ya jikan mamatan sannan ta aika da ta'aziyya ga iyalansu. Ta kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa. ”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta yi kira da a kwantar da hankula sannan ta bukaci mazauna yankin da su guji daukar doka a hannu yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da bincike.

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

Madam Betinah Benson, mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jihar Bayelsa (SSG), Rt. Hon. Konbowei Friday Benson, ta kubuta bayan shafe kwanaki 31 a hannun masu garkuwa da mutane.

Madam Benson, wacce aka yi garkuwa da ita a gidanta da ke tsohon gidan majalisa a Yenagoa a ranar 21 ga watan Yuli, an sake ta ranar Lahadi 22 ga watan Agusta da rana, Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya daga cikin iyali, da ta ki a bayyana sunanta, ta tabbatar da sakin matar mai shekaru 80 amma ba ta bayyana nawa aka biya a matsayin kudin fansa ba ko kuma inda aka sake ta.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Iyalai, 'yan uwa da abokan arziki sun shiga murna da sako Madam Benson da 'yan bindiga suka yi.

Hakazalika, kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat ya tabbatar da sako matar ga jaridar Daily Trust.

Batun kame Sunday Igboho: An ci taran ministan shari'a Malami N50,000 akan Igboho

A wani labarin, Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke zama a Ibadan ta tsawaita umurnin da ta bayar na hana hukumar tsaro na farin kaya daga kame dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho, Punch ta ruwaito.

Mai shari'a Ladiran Akintola, wanda ya bayar da umurnin a ranar 4 ga watan Agusta a zaman da aka ci gaba da yi a ranar Laraba ya kuma ba da umarnin Malami ya biya N50,000 kasancewarsa wanda ake kara na farko.

An ba da umarnin biyan kudin daga Malami ne saboda shigar da martaninsa kan karar da Igboho ya shigar a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Sunayen Matafiya fiye da 20 da aka yi wa kisan gilla a Jos, wani ya rasa 'yanuwansa 7

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.