Zamu Iya Yafe Wa Mayakan Boko Haram da Suka Tuba, Amma da Sharadi, Babban Malami

Zamu Iya Yafe Wa Mayakan Boko Haram da Suka Tuba, Amma da Sharadi, Babban Malami

  • Wani babban malamin coci a Abuja ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan saurin amincewa da tubabbun yan Boko Haram
  • Rabaran Kaigama yace za'a iya yafewa yan ta'addan da suka tuba amma ya kamata gwamnati ta yi taka tsantsan
  • A cewarsa duba da abinda ya faru a kasar Afghanistan na kwace iko, ya kamata a yi adalci

Abuja - Wani babban malamin coci a Abuja, Rev. Ignatius Kaigama, ya gargaɗi gwamnatin tarayya game da yin gaggawar amincewa da tubabbun yan Boko Haram, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Malamin yace za'a iya yafe wa yan Boko Haram ɗin amma ya kamata gwamnati ta yi adalci duba da yanayin da kasa ke ciki.

Rev. Ignatius Kaigama
Zamu Iya Yafe Wa Mayakan Boko Haram da Suka Tuba, Amma da Sharadi, Babban Malami Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kaigama yace:

"Ba zamu taɓa manta wa da abinda yan Boko Haram suka yi na kashe dubbannin mutane da jikkata wasu ba musamman a yankin arewa maso gabas."

Kara karanta wannan

Ba Ni Na Fara Fadin Wannan Maganar Ba, Gwamna Ya Maida Martani Ga Masu Kiran Ya Yi Murabus

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wajibi gwamnati ta yi taka-tsantsan

Malamin cocin yace babban misalin da ya kamata gwamnati ta kalla shine abinda ya faru a ƙasar Afghanistan tsakanin gwamnati da Taliban.

"Misali mafi kusa kan hatsarin mika makamai da yan Boko Haram ke yi, da abinda zai haifar idan ba'a yi taka tsantsan ba shine abinda ya faru a ƙasar Afghanistan."
"Inda yan kungiyar Taliban suka kwace mulkin kasar bayan janyewar sojojin kasar Amurka."

Kaigama ya kuma yi gargadin cewa kada a yi kuskuren sa son rai a shirin canza wa tubabbun yan ta'addan tunani domin su koma rayuwa kamar kowa.

Ya kara da cewa gwamnati ta kula da jin daɗi da walwalar jami'an da zasu gudanar da wannan shirin domin kada a maida abun tamkar kasuwanci.

Kungiyoyin addinai su yi adalci

Malmin ya yi kira ga kungoyoyin addinai kamar MURIC, CAN, JNI da su daina saka son rai a wajen kokarin kare waɗanda suke inuwa ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamna Lalong Ya Roki Al'umma Yafiya Kan Kisan Gillan da Aka Yi Wa Musulmai a Jos

A cewarsa abinda suke yi na kakkausan raddi da nuna wa juna yatsa sam bai dace ba.

A wani labarin kuma An Tsinci Gawar Wata Daliba a Jami'ar Jihar Taraba a Gidan Kwanan Dalibai

Wata daliba a jami'ar jihar Taraba ta rigamu gidan gaskiya a gidan kwanan ɗalibai bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kawayen dalibar sun bayyana cewa ta sha fama da ciwan kai da daddare, amma ta mutu kafin safiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel