Ba Ni Na Fara Fadin Wannan Maganar Ba, Gwamna Ya Maida Martani Ga Masu Kiran Ya Yi Murabus

Ba Ni Na Fara Fadin Wannan Maganar Ba, Gwamna Ya Maida Martani Ga Masu Kiran Ya Yi Murabus

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi watsi da kiran da ake masa ya yi murabus daga kujerarsa
  • Masari yace ba shine gwamna na farko da ya fara ankarar da mutane su kare kansu daga yan bindiga ba
  • A cewar gwamnan duk wanda yake ganin maganar da yayi ta saba to bai ma fahinci halin da ake ciki ba

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi watsi da kiran kungiyar arewa (CNG) na yayi murabus sabida yace mutane su kare kansu daga yan bindiga.

Masari yace ba shine gwamnan farko da ya faɗawa mutane su kare kansu daga ta'addancin yan bindiga ba, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Gwamnan ya kara da cewa kiran da ake masa ya yi murabus daga kujerarsa wata alama ce ta rashin fahimtar halin da kasar nan take ciki.

Kara karanta wannan

Gwanda aikin tukin Keke Napep da koyarwa: Malamar makaranta ta ajiye karantarwa

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari
Ba Ni Na Fara Fadin Wannan Maganar Ba, Gwamna Ya Maida Martani Ga Masu Kiran Ya Yi Murabus Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jihar Katsina na fama da hare-haren yan bindiga, inda suke sace mutane domin neman kuɗin fansa da kuma kashe su ba gaira babu dalili.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa CNG ta nemi Masari ya yi murabus?

Da yake jawabi a wata ziyara da ya kai Jibiya, Gwamna Masari ya bukaci mutanen jihar Katsina su tashi tsaye su kare kansu daga yan bindiga.

A wani jawabi da shugaban ƙungiyar CNG reshen yankin arewa maso yamma, Jamilu Charanci, ya fitar, yace kiran da gwamnan yayi na mutane su kare kansu ya nuna cewa ba shi ke da akalar juya jihar ba.

Charanci ya kara da cewa saboda haka gwamnan ya gaza sauke nauyin da aka ɗora masa na samar da tsaro, don haka ya yi murabus.

Barazana ba zata sa in yi murabus ba

Da yake martani a wani jawabi da kakakinsa, Abdul Labaran, ya fitar, Masari yace wata barazanar tsirarun mutane dake ikirarin kare hakkin dan adam ba zata sanya ya yi murabus ba.

Kara karanta wannan

Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku – In ji Sheikh Ahmad Gumi

Wani sashin jawabin yace:

"A lamarin tsaro, gwamna shine shugaban jami'an tsaro a jiharsa, amma a suna ne kawai saboda shugabannin hukumomin tsaro ba daga hannun gwamna suke karbar umarni ba, daga manyan su na Abuja ne."
"Masari ba shine gwamna na farko da ya fara wannan maganar ba. Duk jihar da mutanenta ba su saka siyasa a lamarin tsaron su ba, zaka samu shugabannin su suna kara musu karfin guiwa."
"Duk wanda yake ganin Masari ya yi murabus kan baiwa jama'ar da yake jagoranta muhimmanci da kara musu karfin guiwar su kare kansu, to sam baima fahimci sakon ba da kuma kundin tsarin mulki."

A wani labarin kuma Mutum 14 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Sake Kai Hari Jihar Kaduna

Akalla mutum 14 suka rasa rayukansu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Mado, karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Maharan sun kone wasu gidaje da dama yayin da suka kai harin ranar Asabar da daddare, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allah ya yadda: Hotunan Jarumi kuma mawaki Garzali Miko tare da zukekiyar matarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel