Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Wata Dalibar Jami'a a Gidan Kwanan Dalibai

Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Wata Dalibar Jami'a a Gidan Kwanan Dalibai

  • Wata daliba a jami'ar jihar Taraba ta rigamu gidan gaskiya a gidan kwanan ɗalibai bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Kawayen dalibar sun bayyana cewa ta sha fama da ciwan kai da dare, amma ta mutu kafin safiya
  • Daraktan yaɗa labarai na jami'ar, Sa'ad Muhammed, ya tabbatar da lamarin, yace zasu yi bincike

Taraba - Wata dalibar jami'ar jihar Taraba dake shekara ta biyu ta rigamu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta tace an garzaya da ɗalibar mai suna Patience Samson Thomas, zuwa asibitin jami'ar ranar Asabar, bayan abokan karatuntu sun gano matsanancin halin rashin lafiyar da take ciki.

Majiyar ta shaida cewa likitocin asibitin sun duba yanayin rashin lafiyanta, sannan suka sallameta a ranar da aka kai ta.

Kara karanta wannan

An kame wani saurayi da ya dirkawa budurwa ciki, ya kashe, ya binne ta a Adamawa

Patience Samson Thomas
Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Wata Dalibar Jami'a a Gidan Kwanan Dalibai Hoto: lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Sai dai majiyar ta kara bayyana cewa ranar Lahadi da safe aka tsinci gawar Samson a dakin kwananta dake gidan kwanan dalibai.

Wata kawarta da suke ɗaki ɗaya, Goodness Emmanuel, tace Patiece ta mutu ne bayan fama da ciwon kai, kamar yadda shafin linda ikeji ya ruwaito

Tace:

"Ta tashi da tsakiyar dare misalin karfe 2:00 tace ciwon kai ya dame ba, daga nan muka fara mata addu'a. Amma ta cika kafin safe."

Jami'ar ta san da mutuwar dalibar?

Daraktan yaɗa labarai na jami'ar jihar Taraba, Sa'ad Muhammed, ya tabbatar da mutuwar ɗalibar ga channels tv a wata tattaunawa ta wayar salula.

Muhammed yace zasu fitar da bayanai game da musabbabin mutuwar dalibar nan gaba.

Hakazalika, shugaban kula da harkokin ɗalibai na jami'ar, Dakta Rebecca Irany, ta kai ziyarar ta'aziyya gidan kwanan ɗalibai.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

A halin yanzun an kai gawar dalibai zuwa sashin ajiye gawarwaki na asibitin jami'ar domin gudanar da bincike.

A wani labarin kuma Bayan Daukar Alkawari, Fulani Sun Tsamo Masu Garkuwa Daga Cikinsu Sun Mikawa Yan Sanda a Taraba

Kungiyar Fulani miyetti Allah ta mika wasu mutum 11 da ake zargin masu garkuwa ne ga hukumar yan sanda.

Kungiyar tace wannan somin taɓi ne a kokarinta na tsame bara gurbi daga cikin fulani a jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262