Rundunar sojojin Najeriya ta damke mai yi wa Boko Haram safarar taki a Yobe

Rundunar sojojin Najeriya ta damke mai yi wa Boko Haram safarar taki a Yobe

  • Sojojin Najeriya sun kama wani mutum da ake zargi da yi wa yan Boko Haram safarar takin zamani
  • Dubun mutumin ya cika ne a kauyen Bayamari da ke karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe
  • Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ta cafke wani Yusuf Saleh, wanda ake zargi da bai wa mayakan Boko Haram safarar takin zamani, jaridar TheCable ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, daga daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, ya ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun cafke wanda ake zargin a kauyen Bayamari da ke karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe.

Rundunar sojojin Najeriya ta damke mai yi wa Boko Haram safarar taki a Yobe
Sojojin Najeriya sun damke mai yi wa Boko Haram safarar taki Hoto: Punch
Asali: UGC

Nwachukwu ya kara da cewa sojojin da ke sa ido sun damke wanda ake zargin da buhuhunan taki 38 (50kg) bayan samun bayanai.

Kara karanta wannan

A karshe ‘yan sanda sun cafke shahararrun masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar Adamawa

Ya ce gwamnatin tarayya ta haramta takin zamani na Urea saboda 'yan ta'adda na amfani da shi wajen kera bama -bamai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, wanda ake zargin a halin yanzu yana taimakawa masu bincike da bayanai masu amfani.

Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa Onyema, ya ambato Babban Hafsan Sojojin yana ba mazauna yankin tabbacin kawo karshen ta’addanci a Arewa maso Gabas.

Ya ce:

“Sojojin da ke sa ido sun cafke wanda ake zargin bayan bayanan da suka samu. Wanda ake zargin a halin yanzu yana taimakawa masu bincike da bayanai masu amfani.”

Hankalin ISWAP ya tashi, sun sauya tsarin shugabanci yayin da Boko Haram ke tuba

A wani labarin, mayakan ISWAP na Najeriya sun canja tsarin shugabancinsu da kungiyar masu basu shawarwari akan yadda mayakan Boko Haram da dama suka zubar da makamansu ga sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, an tumbuke shugabannin ne bisa umarnin hedkwatar ISIS na Iraq da Syria, bisa kasa tabbatar da hadin kan ISWAP da mayakan Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau.

Aba-Ibrahim ne ya maye gurbin Abbah-Gana wanda aka dauka a matsayin shugaban ISWAP, sai Malam Bako, Abdul-Kaka wanda aka fi sani da Sa’ad, Abu Ayun da Abba Kaka, su ne sababbin wadanda aka dauka a kungiyar masu bayar da shawara na ISWAP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng