'Yan sanda a Katsina sun damke mai baiwa 'yan bindiga bayanan sirri
- Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 40 da ake zargin mai baiwa ‘yan bindiga bayanai ne
- Kakakin hukumar, SP Gambo Isah ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a jihar Katsina
- An kama mutumin a ranar 12 ga watan Augusta yana tattaunawa da shugaban masu garkuwa da mutane, Ado Buji ta waya, hakan yasa ake zarginsa
Katsina - Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta damki wani mutum mai shekaru 40 wanda ake zargin mai baiwa masu garkuwa da mutane bayanai a karamar hukumar Faskari dake jihar.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin hukumar, SP Gambo Isah ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a Katsina.
An kama mutumin yana tattaunawa da Ado Buji
A ranar 12 ga watan Augusta, an ji mutumin mai shekaru 40 wanda mazaunin kauyen Godiya ne a karamar hukumar Faskari, yana tattaunawa da shugaban ‘yan bindiga, Ado Buji ta waya sakamakon haka ne yasa jama’an gari suka zargi yana baiwa ‘yan ta’addan bayanai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da aka tsananta bincike, wanda ake zargin ya bayyana yadda ‘yan bindigan suka zazzaga masa N800,000 don ya siya masa kayan masarufi.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa akwai wani mutum mai shekaru 35, mazaunin kauyen Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari wanda shine ya gabatar wa shugaban masu garkuwa da mutane, Buji. Daga baya an bi sawunsa kuma an kama shi.
Ya kuma bayyana yadda yake yi wa masu garkuwa da mutane cefane kuma har N200,000 daga hannun Buji,” a cewarsa.
A cewarsa hukumar ta kama wani tsohon mai laifi wanda yayi karyar jami’in NCS ne yayin da yake satar babur, Daily Nigerian ta ruwaito.
Hukumar ta kama mutumin mai shekaru 32 dan Yamawa Quarters ne a Katsina, wanda dama tsohon mai laifi ne wanda ya shahara wurin balle gida da satar babura.
Yayin bincike an kama wasu da ake zargn sun saci babura 5 kuma aka samu nasarar samun baburan a hannunsu. Har yanzu ana cigaba da bincike,” a cewarsa.
Bata-gari sun sheke mai POS bayan yi mishi fashin N4m a Ogun
Jami’an hukumar ‘yan sanda sun kama mutane 4 da ake zargin suna da hannu da yi wa wani mai POS, Abiodun Odebunmi, fashin naira miliyan 4 kuma daga baya suka hallaka shi kuma suka babbaka gawarsa.
Wadanda ake zargin sune wani Kehinde Saliu Jelili (wanda akafi sani da Oluomo), Abiodun Akinola, Johnson Fakeye da Jamiu Akinola, wadanda aka ce sun yi fice a wurin fashi da hallaka masu POS da UBER.
An kama dukansu bayan wata Aanu Salaudeen ta mika korafinta ga ofishin ‘yan sandan dake Onipanu a ranar 18 ga watan Afirilun 2021.
Asali: Legit.ng