Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma

Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma

  • An fara gudanar da shagalin bikin mika wa Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma
  • Bikin na gudana ne a yau Asabar, 21 ga watan Agusta a masarautar Bichi
  • Tuni manyan baki irinsu, Sarkin Musulmi, Sarkin Kano da Shehun Borno suka isa wajen taro

Surukin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, zai amshi sandar girma a yau Asabar, 21 ga watan Agusta.

Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan daura auren ‘yarsa, Zahra Bayero da dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari.

Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma
An fara bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa tuni aka fara bikin wanda ke gudana a Masarautar Bichi da ke Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa Sarkin Kano bai halarci daurin auren Yusuf da Zahra ba, Kachallan Kano

Zuwa yanzu daga cikin manyan baki da suka hallara a wajen akwai Sultan na Sokoto kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.

Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Har ila yau, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda yakasance ɗan uwan sarkin na Bichi ya hallara a wajen bikin bayan rashin halartar ɗaurin Zarah da kuma Yusuf a ranar Juma'a, 20 ga watan Agusta.

Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Hakazalika mai alfarma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai ya hallara a wajen taron.

Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma
Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Sauran sune Sarakunan Zazzau, Amb Ahmed Nuhu Bamali, na Daura Umar Farouk Umar, Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Lafiya, da mataimakin gwamnan Zamfara, da sauran su, Daily Trust ta ruwaito.

An tsaurara matakan tsaro tun daga mashigar garin tare da jami'an tsaro daban -daban da ke kokarin tabbatar da doka da oda.

Dalilin da yasa Sarkin Kano bai halarci daurin auren Yusuf da Zahra ba, Kachallan Kano

A baya mun kawo cewa Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, bai halarci daurin auren diyar kaninsa Sarkin Bichi, Nasiru Bayero, da aka daura a garin Bichi ba ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce

Wannan abu ya janyo cece-kuce tsakanin jama'a inda wasu suka fara raye-rayen cewa akwai rashin jituwa tsakanin sarakunan biyu.

Majiyar Daily Nigerian ta bayyana cewa Sarkin Kano ya bukaci Sarkin Bichi a daure auren a fadar Kano, amma Sarkin Bichi bai yarda ba.

Amma Kachallan Kano, Magaji Galadima ya bayyana cewa lamarin ba haka bane, Sarakuna ba sa halartan daurin aure ko da kuwa na 'yayansu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel