Dalilin da yasa Sarkin Kano bai halarci daurin auren Yusuf da Zahra ba, Kachallan Kano

Dalilin da yasa Sarkin Kano bai halarci daurin auren Yusuf da Zahra ba, Kachallan Kano

  • Wani mai sarauta a fadar sarkin Kano ya bayyana dalilin da ya sa Sarki Aminu Bayero bai halarci auren Yusuf da Zahra ba
  • Mutane a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun yi cece-kuce kan lamarin
  • Abin ya kai ga sun fara yada jita-jita kan rashin jituwa tsakanin Sarakunan biyu

Kano - Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, bai halarci daurin auren diyar kaninsa Sarkin Bichi, Nasiru Bayero, da aka daura ranar Juma'a a garin Bichi ba ranar Juma'a.

Wannan abu ya janyo cece-kuce tsakanin jama'a inda wasu suka fara raye-rayen cewa akwai rashin jituwa tsakanin sarakunan biyu.

Majiyar Daily Nigerian ta bayyana cewa Sarkin Kano ya bukaci Sarkin Bichi a daure auren a fadar Kano, amma Sarkin Bichi bai yarda ba.

Amma Kachallan Kano, Magaji Galadima ya bayyana cewa lamarin ba haka bane, Sarakuna ba sa halartan daurin aure ko da kuwa na 'yayansu ne.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Kaduna kan raba kudin fansa, sun kashe juna har mutum 9

Yace:

"Wannan al'ada ce ta hana Sarakuna halartan daurin aure. Babu wani rashin jituwa tsakanin Sarakunan biyu. Sarkin Kano kawai ya girmama al'ada ne."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk da cewa a yau, wasu Sarakuna nan sabawa al'ada saboda wani dalili na siyasa ko wani amfani da zasu samu."

Dalilin da yasa Sarkin Kano bai halarci daurin auren Yusuf da Zahra ba, Kachalla
Dalilin da yasa Sarkin Kano bai halarci daurin auren Yusuf da Zahra ba, Kachallan Kano Hoto: Kumbo Photography
Asali: Twitter

Ya kara da cewa a ranar Asabar, Sarkin Kano zai halarci taron mika sandar mulki gwa Sarkin Bichi.

"Domin tabbatar maka da cewa babu wani rashin jituwa tsakaninsu, mai martaba zai halarci bikin mika sandar mulki ga Sarkin Bichi gobe (Asabar). Saboda al'ada ta amince Sarakuna sun halarci taron."
"Idan zaku tuna, tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II bai halarci daurin auren diyarsa ba duk da cewa a fadarsa akayi."

An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki N500,000

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ne ya daura aure tsakanin 'dan Buhari, Yusuf Buhari, da diyar Sarkin Bichi, Zahra Bayero, a Masallacin kasar Bichi.

Kara karanta wannan

Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce

Yayinda babban attajiri, Alhaji Aminu Dantata, ya bada auren a madadin iyalan Sarkin Bichi; dan uwa kuma babban aminin Buhari, Malam Mamman Daura, ya karba aure matsayin wakilin ango kuma madadin shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel