Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce

Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce

  • Mallam Garba Abu, wani mazaunin garin Bichi ya sake yiwa Yusuf Buhari, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari tayin karin mata
  • Mallam Abu ya ce ba zai damu ba idan Yusuf zai iya auren 'yarsa tare da sabuwar amaryarsa, Zahra
  • Shugaba Buhari da wasu manyan jiga-jigan 'yan siyasa suna masarautar Bichi yayin da Yusuf ke auren burin rayuwarsa a ranar Juma'a, 20 ga watan Agusta

Masarautar Bichi, jihar Kano - Yusuf Buhari, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya auri Zahra, diyar sarkin Bichi Nasir Ado Bayero a ranar Juma'a, 20 ga watan Agusta.

Daurin auren ya nuna farin jinin shugaban kasa yayin da fitattun 'yan siyasa a bangarorin siyasa daban-daban suka mamaye masarautar Bichi don bikin dan shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya dira Kano don halartan daurin auren 'dansa Yusuf

Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce
Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa Yusuf Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu Hoto: Bashir Ahmad, BBC News Pidgin
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, a dai-dai lokacin da ake kammala daurin auren Yusuf a Bichi, wani dattijo dan shekara 70 mai suna Malam Garba Abu, ya yi masa tayin 'yarsa.

A cewar BBC Pidgin, Malam Abu, mazaunin garin Bichi, ya ce yana da diya mace kuma ba zai damu ba idan dan Shugaba Buhari, Yusuf, zai iya aurenta tare da diyar Sarkin Bichi Nasir Ado Bayero.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi martani kan kalaman Mallam Abu

A halin da ake ciki, wasu 'yan Najeriya a Facebook sun mayar da martani kan kalaman Mallam Abu.

Chukwuma Simeon ya ce:

"Kada ku damu zai dawo shekara mai zuwa .. Kawai ku ba shi hutu don hutawa wannan ta farko. Allah ya sanya alkhairi yallabai"

Abdul Sanchø ya ce:

"Kayi amfani da hikima an yi wuff da dan Buhari yi amfani da hankali ka sa 'yar ka ta bi sdan shugaban ma'aikata. Lool."

Kara karanta wannan

Daurin auren Yusuf Buhari: Yemi Osinbajo ya dira garin Kano

Murphy Hills ya ce:

"Ba tare da tunanin ko za a yi mata adalci a matsayin matar aure ba? Wasu daga cikinku iyaye ba ku damu da farin cikin 'ya'yanku ba. Ku dai ku damu da abin da za ku amfana daga baya."

Fani-Kayode ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari

A baya mun kawo cewa Femi Fani-Kayode, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, ya shiga cikin wasu manyan jiga-jigan ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin daurin auren dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wasu hotuna da ya wallafa a kafafen sada zumunta, an ga Fani-Kayode, babban mai sukar gwamnatin Buhari, tare da wasu manyan ‘yan APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel