Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

  • Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida ya bayyana ra’ayinsa kan dalilin da yasa sojojin Najeriya ke samun matsala wajen kawo karshen ta’addanci da ‘yan fashi
  • Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya ce sojoji suna da abin da ake bukata don kawo karshen barazanar tsaro amma abubuwa biyu na kawo cikas ga karfinsu
  • Dattijon ya ce an fadada rundunar sojojin kasar da yawa kuma suna amfani da kayan aikin da suka tsufa

Minna, jihar Neja - Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, ya ce an fadada rundunar sojojin Najeriya da yawa, duk da cewar tana da karfin samun nasara a yakin da take yi da masu tayar da kayar baya da 'yan fashi a arewacin kasar.

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Babangida wanda ake kira IBB ya bayyana hakan a wata hira da aka watsa a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta, a gidan talabijin na Arise.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta
IBB ya ce an fadada rundunar sojin kasar da yawa Hoto: FRANCOIS-XAVIER HARISPE/AFP
Asali: Getty Images

An ambato shi yana cewa:

"Rundunar sojoji, na yi imani, suna da karfin da za su yaƙi wannan 'yan fashi da makami kuma su kawo ƙarshensu. Amma na yarda cewa an fadada su da yawa saboda yawan wurin da yakamata su mamaye.”

Jigon kasar ya kuma bayyana tsufan kayan aikinsu a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da gurɓacewar yaƙin da ake yi da 'yan fashi.

Amma, ya ce daya daga cikin abubuwan da ake bukata don samun nasarar yakin sojoji shine cewa dole ne sojoji su yi imani da abin da suke fada akai.

Ku daina take umarnin kotu, tsohon shugaban kasa a mulkin soja, IBB ya gargadi DSS

A wani labarin, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya roki hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta daina bijirewa umarnin kotu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dattijon ya fadi haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na ARISE a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Abinda Muka Tattauna da Jagoran APC Bola Tinubu a Birnin Landan, Gwamna

Babaginda ya ce dole hukumar wacce aka kirkira a karkashinsa ta daina sabawa umarnin kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng