Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci cikin dare

Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci cikin dare

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Obasanjo ya koka kan yawaitar jama'a a nahiyar Afrika
  • Ya bayyana cewa, hakan na hana shi rintsawa cikin dare, lamarin kuma yana damunsa
  • Ya kuma yi tsokaci kan rashin aikin yi da matasa ke fama dashi a nahiyar ta Afrika a yanzu

Abeokuta - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce karuwar yawan mutanen Afirka na fuskantar mummunan yanayi, yanayin da ya ce, yana hana shi bacci cikin dare.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Obasanjo yayi wannan tsokaci ne a ranar Talata, 17 ga watan Agusta lokacin da yake magana yayin gabatar da rahoton sabuwar kungiyar cigaban Afrika (APG).

Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Obasanjo | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Tsoron Obasanjo

Da yake bayyana tsoronsa ga yawan karuwar mutane, Obasanjo ya ce:

Kara karanta wannan

Hotunan birne Mantu da aka yi cike da kiyaye dokar yaduwar Korona

“Tambayoyi guda uku suna tasowa a raina a duk lokacin da tunanin ban tsoro na yawan mutanen da ke karuwa ya hana ni rintsawa da dare. Tambaya ta farko ita ce: ta yaya za mu ciyar da wannan yawan mutane masu haihawa? ”

Jaridar Daily Sun ta rawaito cewa Obasanjo yayi magana da karfin sa a wurin taron a matsayin shugaban APG.

Ya lura cewa yawan rashin aikin yi na matasa a Afirka na iya canzawa zuwa babban hanyar samu ga dan adam wanda zai fassaru zuwa habaka tattalin arzikin nahiyar.

Na fi kowa sa'a duk fadin Najeriya, in ji tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi

A wani labarin, Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi ya ce Allah ya yi masa baiwar da ba wani dan Najeriya da ya taki irin sa’ar da ya samu, Aminiya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

Tsohon Sarki Sanusi kuma Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wani taron cikarsa shekara 60 a duniya a ranar Asabar 14 ga watan Agusta.

A jawabi Sanusi,idan ya yi duba zuwa ga shekaru 60 da ya yi a duniya, yana shiga halin damuwa da kunci, saboda yadda aka samu koma-baya a bangarorin rayuwa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel