Sheikh Daurawa, Gadon-Kaya, Zarewa sun yi wa Ma'aurata bita a kan zaman aure a ABU Zaria

Sheikh Daurawa, Gadon-Kaya, Zarewa sun yi wa Ma'aurata bita a kan zaman aure a ABU Zaria

  • Cibiyar CILS ta Jami’ar ABU Zaria ta shirya bitar kwana biyu domin ma’aurata
  • An gudanar da wannan bita ne a ranakun Asabar da Lahadi a Kongo, Garin Zaria
  • Aminu Daurawa da Abdallah Gadon-Kaya sun yi magana a wajen wannan bitar

Kaduna - Cibiyar CILS da ke nazarin shari’a da addinin musulunci a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta shirya taron bita game da zamantakewar aure.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa an yi wannan bita ne da nufin bayyana matsalolin da ake fuskanta bayan an yi aure, da kawo hanyoyin magance su.

Yadda aka gudanar da bitar kwana 2 a Kongo

An gudanar da wannan taro ne a jami’ar a ranakun Asabar da Lahadi, 14 da 15 ga watan Agusta, 2021. A karshe an ba mahalarta takardar satifiket ta shaida.

Malaman da suka gabatar da jawabi a wajen taron sun hada da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, Dr. Abdullahi Usman Gadon-Kaya da kuma Dr. Jamilu Zarewa.

Sauran masu bayanin su ne Dr. Mardiyyah Abbas Mashi, Dr. Sa’ad Abubakar da Alkali Dr. Lawal Sule.

Jamilu Zarewa wanda shi ne shugaban shirin USRA a cibiyar CILS, ya bude taron da bayani game da manufofin aure a musulunci da kara mata a ranar Asabar.

Abubuwan da suke jawo zinace-zinace

Dr. Abdallah Gadon Kaya ya yi magana a kan abubuwan da suke jawo zinace-zinace a al’umma.

Daga cikin dalilan da malamin ya kawo akwai aika ‘yan mata neman kudi, rokon samari, rashin aure a kan kari, kallon batsa da haramun, da bayyana ado a fili.

Gadon Kaya yace karancin kunya, wayoyin zamani, cakuda maza da mata da kuma rashin adalci a gidan aure suna cikin abubuwan da ke sababba zinace-zinace.

Menene ke kawo yawan mutuwar aure?

Tsohon shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tattauna ne a kan jerin abubuwan da suke yawan kawo mace-macen aure.

Kadan daga ciki; rashin ilmin aure, karya/yaudara, cin amana, auren dole, zargi/yawan kishi, sauyin rayuwa, kawo sharuda, auri-saki da gaggawar daukar mataki.

Shehin ya koka kan yadda tarbiya ta lalace a Arewacin Najeriya a wannan zamani duk da yawan karatu.

“Ka nemi duk wani Farfesa a Arewa da ya shekara 60 ya kawo maka satifiket din mahaifiyarsa, babu. Amma yau masu Digiri uku suke haifa mana 'yan kwaya!
Dalili saboda jahilai ne suke rainon ‘ya ‘yan masu ilmi, su kuma gwamnati suke yi wa aiki da ilminsu.

Imam Sa’ad Abubakar, Mardiyyah Mashi, da Lawal Sule sun gabatar da takardunsu ne a kan tarbiyyar ‘ya ‘ya, tsabta a gidan aure, da kuma tattalin dukiyar mai gida.

A baya an ji cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi alkawarin gina jami’ar addinin musulunci a mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Premium Times ta ce Sanata Rochas Okorocha ya bayyana shirin gidauniyarsa, Rochas Okorocha Foundation, na gina jami'ar musulunci a Daura, jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel