Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

  • Kungiyar kiristoci ta CAN ta bayyana matsayarta game da kashe musulmai da aka yi a garin Jos
  • Wannan ya biyo bayan sanya dokar hana fita da gwamnatin jihar ta yi da yammacin ranar Asabar
  • CAN ta ce, dole ne jami'an tsari su kamo dukkan masu hannu a wannan mummunan kisa da ya faru

Jos, Filato - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Filato, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya musulmai 25 a hanyar Rukuba, a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar.

Rev. Fr. Polycarp Lubo, shugaban CAN a jihar, ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka aikata danyen aikin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Legit Hausa ta rahoto cewa wasu matasa da ake zargin 'yan Irigwe ne sun kai hari kan motocin bas guda biyar dauke da matafiya Musulmai sama da 90, sun kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

Mista Lubo ya kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a kananan hukumomin Bassa, Riyom, Jos ta Kudu da Barkin Ladi.

Kiristocin CAN sun yi martani kan kashe Muslulmai da aka yi a garin Jos
Taswirar jihar Filato | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewarsa:

“Shugabancin CAN gaba daya ya la’anci wadannan hare-hare tare da rokon jami’an tsaro da su tabbatar da an dawo da zaman lafiya.

CAN ta tura sakon jaje ga iyalan wadanda aka cutar

”Muna jajantawa ga iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu, da kuma wadanda aka raba da muhallansu ko kuma aka yi musu lahani ko wace iri.
"Muna kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta cafke duk wadanda ke da hannu, don kawo karshen kashe-kashen da basu dace ba."

Mista Lubo ya ce kungiyar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe

Kara karanta wannan

Bayan hallaka musulmai sama da 20 a Jos, gwamnati ta sanya dokar hana fita

Kungiyar fafutukar kare hakkin musulmai (MURIC) ta yi kira da a gaggauta kame gaba ɗaya waɗanda suka aikata kisan musulmai matafiya a Jos, inda ta kira su da "Mayakan kiristoci a Jos."

Daily Nigerian ta ruwaito cewa matafiya musulmai 25 wasu sojojin ƙungiyar kiristanci suka kashe a Rukaba, jihar Filato ranar Asabar.

A wani jawabi da daraktan MURIC, Ishaq Akintola, ya fitar, ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa musulmai, tare da kira ga gwamnati ta kame waɗanda suka aikata kisan.

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta yi kakkausan martani kan kisan Musulmai a Jos

A wani labarin, Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, Punch ta ruwaito.

Wasu 'yan ta'adda a ranar Asabar sun kai hari kan jerin gwanon motocin bas da ke dauke da matafiya musulmai, inda suka kashe mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Miyetti Allah, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta na kasa, Baba Othman Ngelzarma, a ranar Lahadi a Jos, ya ce har yanzu ba a san inda wasu matafiyan suke ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.