Na so diyata ta kammala karatunta kafin aure, Sarkin Bichi kan shirin auren diyarsa da Yusuf Buhari
- Saura kwana biyu a aurar dan shugaban kasa da diyar Sarkin Bichi
- Za'a daura auren ne ranar Juma'a a Fadar Sarki dake Bichi, jihar Kano
- Sarkin ya yi tsokaci kan wannan daurin aure da ake shirin yi
Kano - Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya bayyana cewa ya so ’diyarsa, Zahra Bayero, ta kammala karatunta kafin tayi aure.
Zahra Bayero dai za ta auri 'dan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
An shirya daura auren Zahra da Yusuf ne ranar Juma’a, 20 ga watan Agustan 2021 bayan Sallar Juma'a a fadar Sarkin Bichi.
A tattaunawar Sarkin Bichi da jaridar Aminiya, mai martaba ya bayyana yadda yake yanzu da zai aurar da diyarsa zahra.
A hirar, Sarkin yace ya kan shiga wani hali duk lokacin da zai aurar da ’ya’yansa saboda shakuwarsa da su.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ina da kusanci da ’ya’yana sosai, saboda aurar da Zahra ma ba karamin tsaka mai wuya ya saka ni ba, amma Alhamudillah.
“Karamar yarinya ce, shekararta 20 kacal, kuma tana shekarar karshe ne a jami’a inda take karantar Fasahar Zane-zanen gine-gine (Architecture).
“Na so a ce ta samu ta kammala karatunta a jami’a, sannan ta dan zauna da mu ko da kadan ne, amma ba haka Allah ya tsara ba, kuma ba zamu iya canza ikonSa ba, sai dai kawai mu yi musu fatan alheri,”
Sarkin Bichi dai shahrarren dan kasuwa ne kuma yanzu haka shine Shugaban kamfanin sadarwa na 9mobile
Sarkin yace ya sami natsuwa ne daga wani Hadisin Annabi (S.A.W) da yake cewa,
“Duk wanda Allah ya ba ’ya’ya mata har guda uku, ya tarbiyyantar da su har ya aurar da su, zai shiga Aljannah.”
“Wannan shi ne fatana, cewa ta sanadiyyarsu, Allah zai bani Aljannah."
Ayiriri: Hoton Katin bikin Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero ya bayyana
Ana shirye-shiryen shagalin bikin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Gimbiya Zahra Nasir Bayero.
An fara bikin ne tun a makon da ya gabata inda aka fara da wasan Polo tare da wankan amarya, lamarin da ya janyo cece-kuce da maganganu daban-daban daga jama'a.
Asali: Legit.ng