Sanata Rochas Okorocha zai gina Jami’ar musulunci a Mahaifar Shugaba Buhari a Katsina

Sanata Rochas Okorocha zai gina Jami’ar musulunci a Mahaifar Shugaba Buhari a Katsina

  • Sanata Rochas Okorocha ya ce zai gina katafariyar Jami’ar Musulunci a Daura
  • Tsohon Gwamna, Rochas Okorocha ya zabi Daura ne saboda an ba shi sarauta
  • Garin Dauran ce Mahaifar Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari a Katsina

Katsina - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi alkawarin gina jami’ar addinin musulunci a mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Premium Times ta ce Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa gidauniyar nan ta sa, Rochas Okorocha Foundation, za ta yi wannan babban aikin.

Jigo kuma Sanatan na jam’iyyar APC zai kafa wannan jami’a ne a garin Daura, Arewacin jihar Katsina.

Menene dalilin kafa jami’ar Musulunci a Daura?

Isa Halidu ya wakilci Sanatan na yankin Imo ta yamma, Rochas Okorocha, wajen wani taro da aka yi a Daura, a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta, 2021.

Kamar yadda Halidu ya shaida wa jama’a, ‘daliban wannan jami’a da za a kafa, za su samu ilmi da wurin kwana a kyauta ba tare da sun biya wasu kudi ba.

Kara karanta wannan

Wanda ya kashe mutum hudu a hadarin mota ba 'dan Umaru Yar'adua bane, dan Shehu Yar'adua ne

“Saboda Mai martaba Sarkin Daura (Umar Farouk Umar) ya ba ni sarautar gargajiya, don haka zan bada tukwuicin da watakila ba za a taba manta wa ba.”

Sanata Rochas Okorocha zai gina Jami’ar musulunci a Mahaifar Shugaba Buhari a Katsina
Sanatan Imo, Rochas Owelle Okorocha
Asali: Facebook

“Zan gina jami’ar addinin musulunci na zamani a karkashin gidauniyar Rochas Okorocha Foundation, wanda ni da kai na zan kaddamar a garin Daura.”

Sahara Reporters ta rahoto Okorocha ya na cewa zai yi wannan aiki ne saboda masarautar Daura da daukacin jihar Katsina sun nuna masa soyayya da kauna.

Gidauniyar Rochas Okorocha ta saba irin wannan

A cewar Rochas Okorocha, gidauniyarsa ta gina makarantu da abubuwan more rayuwa a Katsina da sauran jihohi, don haka wannan karo ya zabi garin Daura.

Okorocha wanda ya bar kujerar Gwamna a 2019 ya ce zai yi wannan a mahaifar shugaban kasa saboda kokarin da Muhammadu Buhari yake yi wa Najeriya.

Kwanakin baya aka ji Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad III ya na koka wa kan halin da al’umma ke ciki, ya ce abubuwa su na kara birkicewa kullum a kasar nan.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya yi muni yayin da aka nemi shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus ya yi murabus

Sultan ya na ganin karancin abinci ya na haddasa matsalar rashin tsaro. Sa’ad III ya ce muddin mutane suna kwana da yunwa, ba za a samu zaman lafiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel