Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?

Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?

  • A ranar 2 ga watan Augustan 2021, sifeta janar na ‘yan sanda, Alkali Baba ya nada Tunji Disu a matsayin shugaban IRT na ‘yan sanda, matsayin Abba Kyari a da
  • PSC ta dakatar da DCP Abba Kyari bisa umarnin IGP akan zargin yana da alaka da rikakken dan damfarar yanar gizon nan, Hushpuppi
  • Tun bayan nada Disu a sabon mukamin, jama’a suka fara nemo tarihinsa daki-daki inda suka ce an haifes hi a kudu maso yamma a 1960

FCT, Abuja - A ranar 2 ga watan Augusta, sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba ya nada Tunji Disu a matsayin sabon shugaban IRT na ‘yan sanda, mukamin da Abba Kyari ya taba rikewa.

An dakatar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, bisa umarnin IGP akan zargin kullalliyar alaka tsakaninsa da Ramon Abbas, rikakken dan damfarar yanar gizo wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Wadanda suka dauke Mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Bayelsa sun ce a biya fansar N500m

Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?
Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An fara rade-radin cewa Tunji Disu ya isa ritaya

Tun bayan nada Disu a sabon mukamin rahotonni suka fara yawo akansa, inda ake cewa an haife shi a kudu maso yanma a ranar 17 ga watan Afirilun 1960.

Ingantattun gidajen watsa labarai sun bayyana tarihin Disu, a ciki muka samo wasu wadanda zamu bayyana a labarin nan.

Yawancin labaran da aka samu akan Disu sun yi kama, kuma akwai alamar gaskiya ne hakan sai dai babu wani kwakkwarar tabbaci akan hakan.

Shin da gaske ne Disu ya kai shekaru 61? Idan haka ne kuwa lokacin murabus din shi ya yi.

Tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya nada shi a matsayin DCP a 2019.

Maganar haihuwar Disu a ranar 17 ga watan Afirilun 1960 yana nuna cewa yanzu haka shekararsa 61, wata 3 da kwana 21 a ranar Litinin, 9 ga watan Augustan 2021.

Saidai bisa sabon tsarin ‘yan sanda wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a Satumban 2020, wajibi mutum yayi murabus idan ya kai shekaru 60 a matsayinsa na dan sanda.

Kara karanta wannan

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

Idan dan sanda ya kai shekaru 35 yana aiki ko kuma ya kai shekaru 60 da haihuwa, wajibi ne yayi murabus ranar zagayowar haihuwarsa.

Kamar yadda aka yi lokacin IGP Mohammed Adamu, CSO sun kira shi don yayi murabus lokacin da ya shiga 60. Shugaba Buhari ya matsa sai ya kai 2023 yana aiki, amma haka nan Buhari ya bi doka ya canja wani IGP din.

Batun Disu kuwa, TheCable tayi magana akai, inda tayi karin bayani akan shi.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Frank Mba, ya sanar da The Cable cewa karya ne maganar haihuwar Disu a 1960 kuma mutane su watsar da maganar.

Akwai rubutattun bayanai na ‘yansanda wadanda suka tabbatar cewa an haifi DCP Tunji Disu a ranar 13 ga watan Afirilun 1966, Mba ya sanar da TheCable ta waya.

Disu ya shiga aikin dansanda a ranar 18 ga watan Yunin 1992 kuma ya kamata ace ya yi shekaru 35 yana aiki yayi murabus a 2026- saidai akwai dokar 'yan sanda wacce ta tilasta murabus da zarar mutum ya kai shekaru 60.

Kara karanta wannan

Ana batun karbar cin hancin Abba Kyari, magajin shi zai karbi kyautar $10,000

DCP din shine kwamandan RRS na jihar Legas daga 2015 zuwa 2020. Kuma ya koma hedkwata yana aiki a 2020 kafin a nada shi shugaban IRT a 2020.

Hukunci

Don haka batun Disu ya isa murabus karya ne, zancen kanzon kurege ne maras tushe balle makama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel