Na fi kowa sa'a duk fadin Najeriya, in ji tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi

Na fi kowa sa'a duk fadin Najeriya, in ji tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi

  • Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana yadda ya taki sa'a a tarihin rayuwarsa
  • A cewarsa, babu wani dan Najeriya da ya taki sa'ar da ya samu a rayuwarsa ta aiki da rayuwa
  • Ya bayyana haka ne yayin bikin tattaunawa ta cikarsa shekaru 60 wanda aka gudanar ranar Asabar

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi ya ce Allah ya yi masa baiwar da ba wani dan Najeriya da ya taki irin sa’ar da ya samu, Aminiya ta ruwaito.

Tsohon Sarki Sanusi wanda kuma shi ne Halifan Darikar Tijjaniyya na Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin wani taron gabatar da makaloli na shekara-shekara da aka gudanar kan cikarsa shekara 60 a duniya a ranar Asabar 14 ga watan Agusta.

A jawabinsa, Sarki Sanusi ya ce idan ya yi waiwaye ya dubi shekaru 60 da ya yi a duniya, yana shiga halin damuwa da kunci, saboda yadda aka samu koma-baya a bangarorin rayuwar Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya koɗa Janar Ibrahim Babangida yayin da ya cika shekara 80 a Duniya

Na fi kowa sa'a duk Najeriya, in tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi
Sanusi Lamido Sanusi | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Ya ce ya zama Shugaban bankin kasuwanci, daga nan ya zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya zama Sarkin Kano, sannan yanzu ya zama Halifan Darikar Tijjaniyya na Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanusi ya ce:

“Babu wani dan Najeriya da ya samu irin wadannan damarmaki da na samu."

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Muhammmadu Sanusi II ya bayyana cewa baya son zama Shugaban kasa ko shiga harkar siyasa, The Nation ta ruwaito.

Don more lokacinsa, tsohon sarkin ya ce ya sami damar shiga Jami'ar London don karatu a shirin PhD a fannin Doka.

Zai yi rubutu kan "Kayyade dokokin iyali na Musulmi, kayan aikin gyara zamantakewa".

Da yake jawabi a wajen liyafar karrama shi don murnar cikarsa shekaru 60 a Abuja, Sanusi ii ya ce tsoro da kwadayi sune manyan abubuwa biyu da suka lalata Najeriya.

Kara karanta wannan

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

Ya ce gogewarsa a gidan yari ta sanya shi rashin jin tsoron zuwa gidan yari ko mutuwa.

Sanusi ya jaddada cewa, kasar na da matsala idan har 'yan Najeriya masu hannu da shuni suka kasa tunanin yadda za su taimaki marasa galihu a kullum.

Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya jinjinawa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda ya bayyana shi a matsayin babban abokin da kowa ya kamata ya samu, DailyTrust ta ruwaito.

Da yake magana a taron maulidin shekara-shekara na Muhammadu Sanusi II a Kaduna, El-Rufai, wanda ya yi magana ta yanar gizo kasancewar yana kasar waje, ya ba da labarin yadda su biyun suka hadu a matsayin dalibai a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Ya ce a wancan lokacin, tsohon sarkin Kano ya fito fili wajen fadin ra’ayoyinsa kuma ya bayyana hangoronsa da burinsa.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel