'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

  • Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa
  • Ya ce, ba siyasa ne a gabansa ba, don haka ya ma koma makaranta zai yi PhD a fannin Doka
  • Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su zama masu tausayawa na kasa dasu shine mafita ga Najeriya

Abuja - Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Muhammmadu Sanusi II ya bayyana cewa baya son zama Shugaban kasa ko shiga harkar siyasa, The Nation ta ruwaito.

Don more lokacinsa, tsohon sarkin ya ce ya sami damar shiga Jami'ar London don karatu a shirin PhD a fannin Doka.

Bani da burin zama shugaban kasa, tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa
Lamido Sanusu II | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Zai yi rubutu kan "Kayyade dokokin iyali na Musulmi, kayan aikin gyara zamantakewa".

Kara karanta wannan

Khalifan Tijjaniyya Ya Magantu Kan Kisan da Aka Yiwa Yan Darikar Tijjaniya Fiye da 20 a Jos

Da yake jawabi a wajen liyafar karrama shi don murnar cikarsa shekaru 60 a Abuja, Sanusi ii ya ce tsoro da kwadayi sune manyan abubuwa biyu da suka lalata Najeriya.

Ya ce gogewarsa a gidan yari ta sanya shi rashin jin tsoron zuwa gidan yari ko mutuwa.

Sanusi ya jaddada cewa, kasar na da matsala idan har 'yan Najeriya masu hannu da shuni suka kasa tunanin yadda za su taimaki marasa galihu a kullum.

Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

Alhaji Muhammad Sanusi, tsohon Sarkin Kano, ya ce Najeriya ba ta samu wani ci gaba ba cikin shekaru 40, tun mulkin shugaban kasa Shagari, Daily Trust ta ruwaito.

Sanusi ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa na murnar cikarsa shekaru 60 a duniya da aka gabatar jiya Asabar 14 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Dan majalisar wakilai mai ci a jam'iyyar PDP ya rigamu gidan gaskiya

Tsohon Gwamnan na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce akwai bukatar ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa.

Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya jinjinawa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda ya bayyana shi a matsayin babban abokin da kowa ya kamata ya samu, DailyTrust ta ruwaito.

Da yake magana a taron maulidin shekara-shekara na Muhammadu Sanusi II a Kaduna, El-Rufai, wanda ya yi magana ta yanar gizo kasancewar yana kasar waje, ya ba da labarin yadda su biyun suka hadu a matsayin dalibai a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Ya ce a wancan lokacin, tsohon sarkin Kano ya fito fili wajen fadin ra’ayoyinsa kuma ya bayyana hangoronsa da burinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.