Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a

Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a

  • Gwamnan jihar Kaduna, ya tuna da yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
  • A cewarsa, abota kamar tasa da ta Muhammadu Sanusi II, ya kamata kowa ya samu irinta a duniya
  • Ya bayyana sarkin a matsayin mutum masanin abin da yake aikatawa kuma mutum mai hangen nesa

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya jinjinawa tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda ya bayyana shi a matsayin babban abokin da kowa ya kamata ya samu, DailyTrust ta ruwaito.

Da yake magana a taron maulidin shekara-shekara na Muhammadu Sanusi II a Kaduna, El-Rufai, wanda ya yi magana ta yanar gizo kasancewar yana kasar waje, ya ba da labarin yadda su biyun suka hadu a matsayin dalibai a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

Ya ce a wancan lokacin, tsohon sarkin Kano ya fito fili wajen fadin ra’ayoyinsa kuma ya bayyana hangoronsa da burinsa.

Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a
Gwamnan jihar Kaduna | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya kasance mai fara'a ta zamani da ci gaba tare da tunani mai kyau wanda ya bayyana a cikin zubin yadda ya bayyana kansa.
"Wadannan halayen sun kasance tare da shi a cikin shekarun da suka gabata, yana da karfin hali kuma yana tunani cikin aiki, an san shi a matsayin daya daga cikin mafi kyawun wannan kasar da ta samar."

Gwamnan ya ci gaba da cewa, tsawon shekarun da suka yi na abokantaka suna nuna kauna ga junansu da kuma sadaukar da kai ga kuma bayyana gaskiya ga juna.

Ya bayyana Sanusi a matsayin wanda ya yi fice a matsayinsa na malami, ma'aikacin banki kuma mai gudanarwa duk rintsi daidai gwargwado a lokacin da ya kai shekaru 40, ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

"Daga nan ya ci gaba da zama Babban Ma'aikacin Banki mai daraja ta duniya, sarki mai kawo sauyi kuma fitaccen malamin addinin Islama.
"A matsayinsa na masani kan ayyukan jama'a, ya kebanta da tunani mai kyau don ci gaban Najeriya, hangen nesa na zabin tattalin arziki da wayewa wajen jagoranci na jama'a."

Cikin dariya, gwamnan ya bayyana yadda Sanusi II ke yawan magana kan yadda shi (El-Rufai) ke sa shi ya zama kamar matsakaici.

Gwamnan ya gode masa saboda abokantakarsu da hidimar da yake yi wa Najeriya gami da Al'ummar Musulmi a matsayin babban jigo kuma Khalifa na darikar Tijjaniyya.

Ba zan taba barin Gwamna El-Rufai ya shigo gidana ba, Sheikh Dahiru Bauchi

Duk da cewa akwai alaka mai karfi tsakanin Sanusi da Tijjaniya, fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi, yace babu dalilin da zai sa ya bar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai ya shiga gidansa idan da ya biyo tawagar tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari suna kangeshi da masu fada masa gaskiya, Dalung

Idan za mu tuna jami'an jihar Kaduna dake tabbatar da yaki da bara sun shiga makarantar malamin inda suka kwashe almajirai a shekarar da ta gabata, Vanguard ta wallafa.

Sheikh Bauchi ya sanar da hakan ne a gidansa dake Bauchi a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin tsohon sarkin wanda aka nada Khalifan Tijjaniya a Najeriya.

MURIC: Gwamna Zulum ya sake gina wasu coci-coci guda 9 da Boko Haram ta lalata

A wani labarin, Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta Muslim Rights Concern (MURIC), ta sake caccakar masu suka da zargin gwamnatin jihar Borno da rashin yi wa Kiristoci adalci, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan rushe cocin EYN da aka yi a makon da ya gabata a Maiduguri, babban birnin jihar, da yawa sun soki gwamnatin jihar bisa wannan aiki.

Sai dai, MURIC, a ranar Talata, ta ce bincike ya nuna cewa gwamnatin jihar ta rusa masallatai fiye da coci-coci, sabanin ikirarin cewa wuraren ibada na kirista ne kawai aka rusa.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

Asali: Legit.ng

Online view pixel