Abun Farin Ciki: Gwamna Zulum Ya Jagoranci Sanya Marayu 5,361 Makaranta a Monguno

Abun Farin Ciki: Gwamna Zulum Ya Jagoranci Sanya Marayu 5,361 Makaranta a Monguno

  • Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya jagoranci sanya marayu makaranta a garin Monguno
  • Zulum wanda ya ɗauki bayanan marayun da kansa, ya ɗauki nauyin basu duk abinda ake bukata kyauta
  • Hakazalika, Zulum ya yi alkawarin sanya wasu yara makaranta waɗanda iyayensu suka bukaci hakan

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ranar Laraba a garin Monguno, ya jagoranci saka marayu 5,361 da rikicin Boko Haram ya kashe iyayensu a makaranta.

Zulum wanda dakansa ya jagoranci ɗaukar bayanan Marayun, ya shafe kwanaki biyu yana gudanar da aikin.

Wannam na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na kafar sada zumunta Facebook.

Gwamna Zulum yayin da yake ɗaukar bayanan Marayu a Monguno
Abun Farin Ciki: Gwamna Zulum Ya Jagoranci Sanya Marayu 5,361 Makaranta a Monguna Hoto: The Governor Of Borno FB Fage
Asali: Facebook

Marayun waɗanda shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 13 za'a ɗauki nauyin kayan makarantarsu, kayan karatu da kuma basu abinci duk kyauta.

An yiwa marayun rijistar makaranta a gaban makusantansu, waɗanda suka bada bayanai game da su da suka haɗa da garuruwan da suka fito da kananan hukumominsu.

Shin su kaɗaine marayun da gwamnati zata ɗauki nauyi?

Waɗanda aka sanya makarantar wani bangare ne na yara 50,000 da rikicin Boko Haram ya maida marayu ko aka nemi iyayen su aka rasa sanadin harin yan Boko Haram tun shekarar 2009.

Wasu iyaye sun nemi Zulum ya haɗa da 'ya'yansu

Duk da cewa shirin na marayu ne kaɗai, amma wasu iyaye a garin sun kawo yayan su, inda suka nemi a sanya su a makaranta.

Bayan wannan bukata ta wasu iyaye ne, Gwamna Zulum ya yi musu alkawarin zai duba kuma ya amince nan gaba.

Gwamna Zulum yace:

"Muna kira ga makusantan waɗannan marayu da aka sanya a makaranta da su taimaka mana wajen sanya ido akan yaran, domin tabbatar da suna zuwa yanda ya kamata."

Yayin gudanar da aikin saka marayun makaranta, Zulum ya samu taimakon kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulkarim Lawan, kwamishinoni da kuma manyan jami'an gwamnati.

A wani labarin kuma Ku Bada Wasiyya Kafin Ku Fito Daga Gida, Gwamna Ya Gargaɗi Masu Shirin Magudin Zabe a 2023

Gwamna yace idan suka ki kuma to kar su zargi kowa su zargi kansu a kan duk abinda ya faru da su lokacin zaben 2023.

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne yayin zantawa da manema labarai a Makuɗi jim kaɗan bayan dawowarsa daga taron gwamnonin PDP a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel