Ku Bada Wasiyya Kafin Ku Fito Daga Gida, Gwamna Ya Gargaɗi Masu Shirin Magudin Zabe a 2023
- Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya gargaɗi masu shirin maguɗin zaɓe a jihar da su bar wasiyya kafin fitowa gida
- Gwamnan ya faɗi haka ne yayin zantawa da manema labarai a Makurdi jim kaɗan bayan dawowarsa daga Abuja
- APC reshen jihar Benuwai tace maganganun gwamnan na nuni da wata makarkashiya da ake shiryawa
Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya gargaɗi duk wasu masu shirin maguɗin zaɓe a 2023 da su fice daga jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamna yace idan suka ki kuma to kar su zargi kowa su zargi kansu a kan duk abinda ya faru da su lokacin zaben 2023.
Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne yayin zantawa da manema labarai a Makuɗi jim kaɗan bayan dawowarsa daga taron gwamnonin PDP a Abuja.
Menene matsayarku kan tura sakamako ta Na'ura?
Gwamna Ortom yace Najeriya ta kai duk matakin da ya kamata kuma bai kamata a cigaba da harkar zaɓe a rubuce ba kamata ya yi a fara amfani da fasahar zamani.
Leadership ta rahoto a jawabinsa, Ortom yace:
"Ya kamata shugaban ƙasa ya sake tunani, ina mai ba shi shawara kada ya sanya hannu a kan dokokin zaɓe da aka yiwa garambawul ba tare da an sanya tura sakamako ta na'ura ba."
"Mu anan jihar Benuwai mun kammala shiri, duk wanda ya zo zai mana maguɗin zaɓe a 2023, to ya bar wasiyya tun kan ya fito gida.
"Babu wanda zai zo ya canza mana sakamakon zaɓe ba cin mu ne mafiya rinjaye, ba zai taɓa yuwuwa ba."
Wai meyasa PDP batasan komai ba sai maguɗin zaɓe?
Da yake martani ga gwamnan, Kakakin jam'iyyar APC reshen jihar, James Ornguga, yace Ortom da jam'iyyarsa ba su san komai ba sai maguɗin zaɓe.
James yace
"Idan babu maguɗi, gwamna Ortom da jam'iyyarsa ta PDP ba zasu iya kai bantensu ba a kowane zaɓe a jihar Benuwai."
"Wannan karon APC dai-dai take da shi, domin ba zamu sake bari ya yi maguɗin zaɓe ba a jihar Benuwai. Maganganunsa na nuna wata maƙarkashiya da ake shirya wa."
A wani labarin kuma Mamakon Ruwan Sama Ya Cinye Mutum 5, Ya Yi Kaca-Kaca da Gonakin Al'umma 1,567 a Bauchi
Mamakon ruwan wanda aka shafe sama da awanni 20 ana yi, ya lalata amfanin gonakin mutane a ƙauyuka 7 dake yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar Jama'are, Sama'ila Jarma, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Asali: Legit.ng