Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

  • Bright Ben ya zargi faston cocin da ya yi imani da ita cewa ya kwace masa matarsa
  • Matar mai suna Tina, ta musanta ikirarin Bright, inda tace sun rabune ta tsiya yana wulakantata
  • Mahaifiyar Tina, ta bayyana cewa tsohon mijin ɗiyarta Bright bai biya kuɗin sadaki ba har yanzu

Rivers - Wani mutumi, Bright Ben, ya zargi babban faston cocin su ta General Overseer dake Eneka, karamar hukumar Obio-Akpor, jihar Rivers da yi masa kwacen mata.

Bright ya bayyana cewa lamarin ya fara ne daga lokacin da aka baiwa matarsa da sukai shekara 12 tare mukamin mai hidima ga coci.

Yace tun daga wannan lokacin matarsa mai suna Tina, ta tattara kaya ta bar gidansu tare da 'ya'yan da suka haifa guda biyu.

Tina da Bright, da kuma Tina da Fasto
Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai da na nemi shawarar Faston kan ɓatar matata

Bright yace ya jima yana neman inda matarsa ta koma kuma sai da ya kira faston nasa domin neman shawara kan lamarin.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Gwamnan New York Ya Yi Murabus Kan Zargin Cin Zarafin Mata

Ya kara da cewa daga baya sai ya gano inda ta koma ranar Lahadi yayin da yaga kyawawan hotunanta ta sake wani auren na daban.

Shin wannan abun kunya ne?

Bright, a wani rubutun takaici da yayi a shafinsa na Facebook, yace wannan auren na malaminsa da matarsa babban abun kunya ne.

A rubutunsa, Bright yace:

"Malamin coci na ya auri matata. Mun kasance ma'aurata da Tina shekaru 12 da suka gabata. Na gabatar da ita ga faston nawa daga nan muka cigaba da halartar cocin tare."
"Ba da jimawa ba a ka baiwa matata mukamin mataimakiya a cocin watanni 7 da suka shuɗe, watarana kawai sai ta tattara kaya tabar gidana lokacin ina wurin aiki.
"Na neme ta a ko ina kuma na kira duk wanda ya dace har da faston cocin namu domin shike maganin matsalolina. Amma bayan wani lokaci sai ya daina daga kiran wayata."

Kara karanta wannan

Abin kunya ne a ce Buhari dan Arewa ne, 'yan Arewa sun soki mulkin Buhari

"Na jima ina nemanta har sai da na ga hotunanta akafar sada zumunta, faston ya yi ikirarin ubangiji ne ya faɗa masa cewa matarsa ce."

Tina ta maida martani ga Bright

A martani da ta yi a kafar sada zumunta, Tina, ta bayyana cewa ta fece ta bar mijinta ne saboda cin zarafinta da yake yi da kuma rashin kulawa.

A rubutun ta, Tina tace:

"Tsohon mijina yaso maida ni matar banza a kafar sada zumunta, lokacin da muke tare yasa na ciyo bashi wanda har yanzun ban kammala biya ba."
"Ya hana ni cika burina na zama mawakiya, kai daga baya ma ya faɗamun cewa babu aure tsakanin mu, ina zaune ne kawai domin kula masa da ƴaƴan mu."
"Yayi alkawarin lalata rayuwata, amma yanzun yazo kafar sada zumunta yana kokarin ɓata wa wani suna. Nima lokacina ne nayi abinda raina ke so."

Tina ta kara da cewa karya yake yace baisan inda nake ba domin na bar gidan shi ne bayan ya kulle ni a ɗaki ya tafi da makullan.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

Tina da sabon Angonta
Babban Malamin Addini Ya Kwace Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure Hoto: Bright Ben FB fage
Asali: Facebook

Bright bai biya sadakin Tina ba

Mahaifiyar Tina, Christiana Everest, ta bayyana cewa mijin diyarta na farko bai biya sadakin auren su ba har yanzun.

Ta bayyana cewa Bright ya baiwa kowa hakkinsa maza da mata na iyalan gidan mu amma banda iyayen Tina.

Tace duk lokacin da aka ce masa ya kai wa iyayen amaryar tasa ziyarsa sai yace ba yanzun ba zai je daga baya.

Dagaske zargin da ake maka ka aikata?

Bright a ya musanta duk wasu zarge-zarge na cin mutuncin matarsa da aka ɗora masa.

Hakazalika ya musanta zargin da mahaifiyar tsohuwar matar tasa ta masa cewa bai biya sadaki ba, inda ya kara da cewa ya yi komai lokacin bikin al'ada.

A wani labarin kuma wasu yan Najeriya sun maida raddi ga mayakan Boko Haram da suka nemi a yafe musu halin tasku da suka jefa mutane.

A makon da ya gabata ne rundunar soji ta sanar da sama da mutum 100 sun mika makamansu.

Kara karanta wannan

Asadul-Islam, Datti Assalafy sun yi mun kazafi iri-iri, wasu cewa sukayi mijina ba Musulmi bane: Aisha Yesufu

Yan Najeriya sun ce ba zasu taba yafe musu ba dole ne su fuskanci hukunci kan abinda suka aikata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel