Abin kunya ne a ce Buhari dan Arewa ne, 'yan Arewa sun soki mulkin Buhari

Abin kunya ne a ce Buhari dan Arewa ne, 'yan Arewa sun soki mulkin Buhari

  • Kungiyar tuntuba ta Arewa ta ce shugaba Buhari ya kasance abin kunya ga 'yan Arewa
  • Kungiyar ta bayyana haka ne yayin da ta ke koka yadda gwamnatin ke tafiya ta fannin tsaro
  • Kungiyar ta kuma bayyana yadda tuntuni take nuni da cewa, gwamnatin ta gaza wajen magance matsalolin tsaro

Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta bayyana shugaba Buhari a matsayin abin kunya ga Arewa, kasancewar ya gagara komai kan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta, musamman arewacin Najeriya.

Mr. Emmanuel Yawe, sakataren yada labarai na kungiyar ne ya bayyana haka yayin wata hira da jaridar Daily Sun da aka wallafa ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, inda ya ke mamakin yadda shugaban ya kasance tsohon soja amma ya kasa tabuka wania abin kirki.

Mr. Emmanuel ya bayyana yadda kungiyar ta ACF ke nuna damuwarta game da yadda kasar nan ke ciki, yana mai cewa, Arewa ta kasance cikin firgici, sannan babu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

A haramta haska shirin Big Brother Naija: Kungiyar Arewa sun bukaci gwamnatin Najeriya

Abin kunya ne a ce Buhari dan Arewa ne, kungiyar Arewa ta soki mulkin Buhari
Kungiyar Tuntuba ta Arewa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yayin da aka tambaye shi irin damuwar da ACF ke ciki game da yawaitar tashe-tashen hankula a Arewa, Mr. Emmanuel ya ce:

"Ka san muna matukar nuna damuwa game da yanayin tsaro a kasar fiye da kima yayin da mutumin da yake shugaban kasa ba kawai janar ne na yaki kadai ba, tsohon Shugaba ne na mulkin Soja a baya.
"Ta yaya za ka ba da shawara ga gwamnatin da wani mutum ke jagoranta wanda yake da tsohon tarihin aikin tsaro?
"Wasu daga cikin mu da suka taka rawar gani a lokacin da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2015 mun ji cewa abin da ke faruwa a halin yanzu ya kai abin kunya matuka."

ACF ta jima da gane Najeriya na cikin mummunan hali

Da yake sake jaddada yadda matsalolin kasar ke kara hauhawa, Mr Emmanuel ya ce, ACF ta jima tana fadin cewa, halin da Najeriya ke ciki na muni ya ta'azzara.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

A kalamansa kamar yadda yazo a Daily Sun, cewa ya yi:

"Mun fada da babbar murya cewa yanayin tsaro ya munana. Mun fadi hakan, ba a boye ba cewa 'yan Najeriya musamman 'yan Arewa ba su da kwanciyar hankali. Abin da ya kamata a yi shi ne siyasa ta shawo kan lamarin.
"Abin takaici, gwamnatocin jihohi da na tarayya, sun gaza a kan wannan. Duk mun san akwai wata hadaka da ta mamaye kungiyoyin farar hula, sojoji, majalisa da zartarwa wadanda basa son ganin karshen wannan rashin tsaro.

Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari

A wani labarin, Cece-kuce ya barke tun bayan wani tattaunawa da aka yi da tsohon shugaban kasa na mulkin soji a ARISE TV inda yace mulkinsa ya yi yaki da cin hanci da rashawa fiye da mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

IBB ya tunatar da yadda ya sauke gwamna akan satar N313,000 amma a halin yanzu mutane da dama da suka saci biliyoyin nairori suna yawonsu a cikin kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Wannan furucin nashi ya janyo cece-kuce, wasu suna sukar maganarsa yayin da wasu suka amince da maganarsa inda suke cewa rashawa tana kara yawaita a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel