Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

  • A karon farko, mai magana da yawun Badamasi Babangida, Prince Kassim Afegbua, ya magantu a kan haɗarin da yake fuskanta
  • Jigon na Jam'iyyar PDP bai bayyana ko ya kai kara ga 'yan sanda ba
  • Dan siyasar ya bayyana dalilin da ya sa yake fuskantar barazana daga wasu mutane da ba a san ko su wanene ba da kuma yadda ya magance lamarin

Prince Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bayyana cewa sau biyu yana tsallake rijiya da baya daga yunkurin kashe shi.

Tsohon kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar Edo ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The Nation wanda aka wallafa a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta.

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua
Afegbua ya ce ya ga rayuwa Hoto: Prince Kassim Afegbua
Asali: Facebook

Kodayake Afegbua bai yi cikakken bayani game da yunƙurin da aka yi na kashe shi ba, amma ya bayyana cewa waɗancan yanayin sun kusa kai shi ga mutuwa.

Kara karanta wannan

A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

Dan siyasar ya ce yana da tabo a duk jikinsa biyo bayan hare-haren. Afegbua ya bayyana cewa har yanzu yana samun barazana saboda ya kasance mai sukar gwamnati ne.

Ya ce:

“Har yanzu akwai barazanar saboda ina sukar gwamnati da rashin yin abin da ya dace. Ina tausayawa talaka. Na tsani ganin yadda mutane ke shan wahala saboda na san halin da na shiga kafin na kai wannan matsayin."

Jigon na jam'iyyar PDP ya kuma bayyana Babangida a matsayin mutum mai hazaka, mai iya magana.

IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

A wani labarin, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da “evil genius” wato "mugun gwani" da "Maradona".

Babangida, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Arise TV a wata hira da jaridar The Nation ta sa ido a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki

Ya bayyana cewa kafafen yada labarai ne suka kakaba masa wannan sunan saboda "ƙaƙƙarfan salon siyasarsa".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng