Ba Zamu Taba Yafe Muku Ba, Martanin Yan Najeriya Ga Kwamandojin Boko Haram da Suka Tuba

Ba Zamu Taba Yafe Muku Ba, Martanin Yan Najeriya Ga Kwamandojin Boko Haram da Suka Tuba

  • Wasu yan Najeriya sun maida martani ga yan Boko Haram da suka tuba suka nemi a yafe musu
  • A makon da ya gabata ne rundunar soji ta sanar da sama da mutum 100 sun mika makamansu
  • Yan Najeriya sun ce ba zasu taba yafe musu ba dole ne su fuskanci hukunci kan abinda suka aikata

Abuja - Sama da kwamandoji 100 ne suka tuba suka mika makamansu ga sojojij Operation Haɗin Kai na rundunar sojin kasa.

Manyan yan ta'addan sun mikamakansu domin rungumar zaman lafaya tare da neman yan Najeriya su yafe musu kuskuren da suka yi a baya.

Wannan matakin tuba da yan Boko Harama suka ɗauka da kuma shirin da gwamnatin tarayya take yi na canza musu tunani su koma cikin jama'a tare da mutane ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Vanguard ta ruwaito wasu na korafin cewa ta ya za'a yi yafe wa yan ta'adda amma masu fafutukar ballewa na shan tsangwama.

Kara karanta wannan

A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya

Tubabbun yan Boko Haram
Ba Zamu Taba Yafe Muku Ba, Martanin Yan Najeriya Ga Kwamandojin Boko Haram da Suka Tuba Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dagaske yan tubabbun yan Boko Haram sun nemi yafiya?

Lokacin da sojojin Operation Haɗin Kai suka tara tubabbun yan tada kayar bayan a sansaninsu na jihar Borno, sun ɗaga katin dake nuna neman yan Najeriya su yafe musu.

Wasu daga cikin takardun da suka ɗaga an rubuta "Dan Allah yan Najeriya ku yafe mana", "Har yanzun ansan jihar Borno da zaman Lafiya" da sauransu.

Me yan Najeriya suka ce?

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin martanin yan Najeriya a kafafen sada zumunta.

Ibeachu Kenneth yace:

"Daga baya za'a iya ɗaukarsu aikin soji da sauran hukumomin tsaro kuma a tura su yankin gabas su yaki masu son kafa kasar Biyafara."

Richard O Richard yace:

"Ina tausayawa iyalan waɗanda aka kashe, shikenan sun rasa yan uwansu har abada."

Pablo Martini yace:

Kuna neman yafiya a gurin waɗanda kuka kashe ko su waye kuke so su yafe muku? Najeriya tana da abun mamamki sosai.

Kara karanta wannan

Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga

"Ana yafe wa yan ta'adda amma a ɓangare ɗaya kuma ana kashe masu zanga-zangar zaman lafiya."

Abdulhafiz Marwa yace:

"Ba zamu taɓa yafe muku ba."

Jude Destiny yace:

"Sam babu maganar yafe muku, ya zama wajibi ku fuskanci hukunci."

A wani labarin kuma tsohon ministan wasanni ya caccaki ma'aikatar wasanni game da gasar Olmypics 2020

Barista Salomon Dalung ya bayyana cewa ma'aikatar ta kunyata Najeriya a idon Duniya, kuma dama can yawon buɗe ido suka je ba buga wasa ba

Dalung yace babu yadda za'a yi a rushe hukumomin da suka ɗau shekaru suna shirya yan wasa kuma a yi tunanin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262