Zargin cin hanci: Gwamna Zulum ya ce shi kam bai san hanyar gidan Abba Kyari ba

Zargin cin hanci: Gwamna Zulum ya ce shi kam bai san hanyar gidan Abba Kyari ba

  • Gwamnan jihar Borno ya karya bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya taba zuwa gidan Abba Kyari
  • Gwamnan ya ce shi bai ma san hanyar gidan Abba Kyari ba balle ma ace ya taba zuwa gidansa
  • Ya yi bayanin dalla-dalla inda aka dauki bidiyon tare da yin tsokaci kan yadda suka hadu a wani wuri

Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya karyata jita-jitan da ke yawo cewa ya taba zuwa gidan Abba Kyari, yana mai cewa, bai ma san hanyar gidan Abba Kyari ba.

Wannan na zuwa ne yayin da wani bidiyo ya shahara a kafafen sada zumunta cewa , gwamna Zulum ya ziyarcu gidan Abba Kyari a wani lokaci.

Mai magana da yawun gwamna Zulum, Malam Isa Gusau ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da gwamna Zulum ya yada a shafinsa na Facebook a ranar Laraba 4 ga watan Agusta, 2021.

Gwamnan ya bayyana gaskiyar inda aka dauki bidiyon, yana mai karyata cewa, bidiyon ba a gidan Abba Kyari aka dauke shi ba.

Zargin cin hanci: Gwamna Zulum ya ce shi kam bai san hanyar gidan Abba Kyari ba
Gwamnan Borno, Zulum | Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

A cewar sanarwar:

"Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da wanda ya gada, Sanata Kashim Shettima ba su san gidan DCP Abba Kyari da ke fuskantar rikici ba, balle su ziyarce shi."

Ta kara da cewa:

"Wasu abokan Abba Kyari sun dauki bidiyon da ke yawo ne a gidan Sanata Kashim Shettima da ke Abuja a ranar 30 ga Yuni, 2021, lokacin da Abba Kyari ya kai ziyarar jajega Shettima sakamakon munanan rade-radin da ake yadawa na cewa Sanatan ya mutu a Birtaniya.
Kyari da kansa ya yada wannan bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar 30 ga Yuni, jim kadan bayan ya ziyarci Shettima.

Ta yaya za a tabbatar da hakan?

Gusau ya kuma yi nuni ga mutane da su sa ido don lura da talabijin din da ke bayan Zulum da Abba Kyari tare da labarai na CNN na dan wasan barkwanci na Amurka, Bill Cosby, a cewarsa, za a iya tabbata da hakan ya faru ne a ranar 30 ga Yuni, 2021.

Gusau ya yi kira ga Abba Kyari da ya bayyana gaskiyar hakan domin karin haske kamar yadda ya yi alkawari lokacin da aka jawo hankalinsa kan labarin cewa Kyari ne da kansa ya dauki wannan bidiyon ya kuma sake shi a shafinsa na Facebook ranar 30 ga Yuni, 2021.

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

A wani labarin, ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel