Gaskiya za ta bayyana, kowa ya san bana karya: Abba Kyari ya sake jaddadawa
- Bayan dakatad da shi, Abba Kyari ya aike sakon godiya ga mutanensa
- Ya jaddada cewa shi mai gaskiya ne kuma gaskiya zata wanke shi
- Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike kan sa
Hazikin dan Sanda, DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar ya jaddada cewa shi fa yana da gaskiya kan tuhumar da ake masa kuma nan ba da dadewa ba gaskiya zai bayyana.
Abba Kyari ya sake magana ne a jawabin da ya daura a shafin yanar gizon tsaffin wadanda suka halarci wani taro a Amurka, ThisDay ta gano.
Yace dukkan abubuwan da ya fada kuma ya daura a shafinsa gaskiya ne.
Wani sashen jawabin yace:
"Ga dukkan abokai ne da abokan aiki na a ofis, kada ku damu. Ina cikin koshin lafiya da ba na cikin damuwa."
"Dukkan wadanda suka san ni sosai sun san ba na son karya. Dukkan abinda na fada ko na wallafa gaskiya ne. Nan ba da dadewa ba gaskiyar lamarin nan zata bayyana."
"Mun godewa Allah bamuyi rashin wani sashen jikinmu a dukkan hare-hare masu haduran da kuma kai ba a fadin tarayya."
Akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili
Shahararren lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan adam, Cif Femi Falana (SAN) ya yi kira ga Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya aiwatar da bukatar Amurka ta mika mata Abba Kyari akan ka'ida.
Kyari, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Borno, kwanan nan ne Hukumar Bincike ta FBI, wata hukumar tabbatar da doka a Amurka ta zarge shi da hannu a wata harkallar damfara.
Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfarar wani hamshakin attajiri, ya furta cewa ya ba Kyari cin hanci don kamo wani da ya nemi ya zarce shi a zambar dala miliyan 1.1.
Asali: Legit.ng