Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

  • Ofishin ministan shari'a a Najeriya ya magantu kan tuhumar da Amurka ke yi wa Abba Kyari
  • Wannan ya biyo bayan dakatar da Abba Kyari bisa zargin karbar cin hanci, wanda FBI ta yi
  • Ofishin ministan ya ce har yanzu bai karbi wata takarda a hukumance da ke neman kame Kyari ba

Abuja - Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, kuma ministan Shari'a Abubakar Malami, ta ce har yanzu ba ta karbi wata takarda a hukumance daga cibiyar binciken Amurka ta FBI ba da ke neman damar kame mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.

Wannan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga ministan, Umar Gwandu yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Punch.

FBI ta zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun Hushpuppi, wani dan damfara dake fuskantar zaman kotu a Amurka, bayan kame masa wani abokin harkallarsa.

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari
Ministan Shari'a, Abubakr Malami (SAN) | Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

Duk da cewa Kyari ya karyata zargin, Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan Sanda ta fara bincike kan gaskiyar lamarin yayin da aka dakatar da Abba Kyari.

Kara karanta wannan

FBI ba ta da ikon kame Abba Kyari, babban lauya Mike Ozekhome ya fadi dalili

Lokacin da aka tambaye shi ko Ofishin AGF ya samu wata takarda daga FBI ko rundunar 'yan sandan Najeriya dangane da sammacin kama Kyari, mai taimaka wa Malami ya ce ba a sanar da ofishin ba.

Ofishin AGF ne ke da alhakin batutuwan da suka shafi mikawa, maida mai laifi gida da canja wuri ga wadanda ake zargi ko wadanda ake nema.

Gwandu ya ce:

"Babu wata hanyar sadarwa a hukumance kan hakan."

Mai taimaka wa AGF ya kuma ce ba za a fara tsarin mika Kyari ba har sai an samu bukatar hakan a rubuce daga Amurka.

Duk da haka, ya ba da tabbacin cewa:

"Komai za a yi shi bisa ga doka kuma bisa dogaro da manyan abubuwan da doka ta tanada".

FBI ba ta da ikon kame Abba Kyari, babban lauya Mike Ozekhome ya fadi dalili

Babban Lauyan Najeriya, Mike Ozekhome (SAN), ya ce tilas Amurka ta gabatar da bukatar neman a mika mata mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari ta hanyar da ta dace.

Kara karanta wannan

Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla

Cibiyar Binciken Manyan Laifuka ta FBI ne ta zargi Kyari a wata tuhumar zamba da Ramon Abbas wanda kuma ake kira Hushpuppi ke fuskanta a Amurka.

Tuhumar Kyari ta biyo bayan umurnin kama shi daga wata kotun Amurka a gundumar tsakiyar California.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Ozekhome ya ce hukumar FBI ba ta da ikon zuwa Najeriya haka kawai don kama Kyari ba tare da bin ka’ida ba.

Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla

A wani labarin, awanni bayan da hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta dakatar da DCP Abba Kyari bisa shawarin Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba, Cibiyar Binciken Manyan Laifuka TA FBI Ta bayyana sabbin bayanai game da Abba Kyari.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, FBI ta yi zargin Abass Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya bai wa Abba Kyari N8m ko $20,600, don kamawa da tsare wani abokin harkallarsa mai suna Kelly Vincent.

Kara karanta wannan

Babban Kamu: FBI ta kwamuso wasu 'yan Najeriya da ke damfara a kasar Amurka

Legit.ng ta tattaro cewa jaridar ta ce batun na cikin takardar da Kotun Amurka ta bayar na gundumar tsakiyar California mai dauke da kwanan wata 12 ga Fabrairu, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel