Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

  • Wata kotu a jihar Oyo ta umarci gwamnatin tarayya da ta dakata da kame Sunday Igboho
  • Kotun ta bayyana haka ne a yau Laraba 4 ga watan Agusta, 2021 yayin zaman sauraran kara
  • Sunday Igboho ya shigar da kara ne kan neman a karba masa diyyar miliyan 500 bisa shiga gidansa

Mai shari’a Ladiean Akintola na babbar kotun Oyo ya hana hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da babban lauyan gwamnatin tarayya kamawa, bincika, tursasawa, da toshe asusun banki na Cif Sunday Adeyemo aka Sunday Igboho, The Nation ta ruwaito.

An bayar da wannan umurnin ne bayan wani tsohon kudiri da lauyansa Cif Yomi Aliu (SAN) ya gabatar a kotun a ranar Laraba.

Wannan ya samo asali ne daga kudirin neman diyyar Naira biliyan 500 saboda mamaye gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar 1 ga watan Yuli.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta ba da umarnin hana AGF da DSS su kame Sunday Igboho
Sunday Igboho | Hoto: channeltv.com
Asali: UGC

Aliu ya bayyana kwarin gwiwa cewa AGF Abubakar Malami (SAN) ba zai yi watsi da umarnin kotu ba, yana mai jaddada cewa an bayar da umarnin ne kai tsaye kan ofishinsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: DSS Ta Bi Umarnin Kotu, Ta Gabatar da Dukkan Hadiman Sunday Igboho a Kotu

An dage sauraren karar zuwa 18 ga watan Agusta.

Sabbin laifukan da ake zargin Igboho da aikatawa

Ibrahim Salami, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Igboho ya bayyana cewa an bijiro da sabbin tuhume-tuhume a kan Sunday Igboho a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, yayin zaman kotu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Wadannan su ne uku daga cikin manyan laifukan da gwamnatin jamhuriyar Benin ke tuhumar Igboho akai:

  1. Hijira ba bisa ka'ida ba
  2. Hadin baki da jami'an shige da fice
  3. Kokarin haifar da tarzoma

Me yasa Igboho ya bar Najeriya?

Me yasa Igboho ya bar Najeriya? Makonni kadan da suka gabata, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta mamaye gidan Igboho da ke Ibadan bayan ta zarge shi da tara makamai, in ji The Cable.

Mamayar ta kai ga kashe wasu mutane biyu na Igboho amma dan awaren Yarbawan ya tsere. Daga baya ne DSS ta bayyana cewa ana neman Igboho.

Kara karanta wannan

FBI: A karshe Abba Kyari ya bayyana a gaban kwamitin bincike na 'yan sanda, ya kare kansa daga tuhuma

An kama Igboho a ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, a tashar jirgin sama ta Cotonou, Jamhuriyar Benin a kan hanyarsa ta zuwa Jamus.

Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

A wani labarin, Sarakunan Yarbawa a Jamhuriyar Benin, a ranar Lahadi, sun gana a kan kamawa da tsare dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

An yi taron ne a Fadar Alajohoun na Adjohoun, wanda ke da tazarar kusan kilomita 60 daga Ajase.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alajashe na Ajase daga Port Novo, Alajohoun na Adjohoun, Onikoyi Abesan, da Oba na Seme.

Asali: Legit.ng

Online view pixel