Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

  • Sarakunan Yarbawa a Benin sun yi taro don tattauna batun tsare wa da kame Sunday Igboho
  • Rahoto ya bayyana sunayen sarakunan da kuma yankunan da suka fito a jamhuriyar Benin
  • A baya an bayyana laifuka da dama da ake zargin Sunday Igboho, kuma a hakin yanzu yana jiran hukunci

Sarakunan Yarbawa a Jamhuriyar Benin, a ranar Lahadi, sun gana a kan kamawa da tsare dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

An yi taron ne a Fadar Alajohoun na Adjohoun, wanda ke da tazarar kusan kilomita 60 daga Ajase.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alajashe na Ajase daga Port Novo, Alajohoun na Adjohoun, Onikoyi Abesan, da Oba na Seme.

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho
Sunday Igboho | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kotun ta Benin ta dage shari’ar Igboho zuwa ranar Litinin (gobe) bayan lauyoyinsa biyar sun kasa shawo kan mai gabatar da kara cewa ba shi da wata hujja da zai amsa.

Lauyoyin sun ce a yayin sauraren karar, masu gabatar da kara sun yi ikirarin cewa Igboho yana cikin jerin masu sa ido kan safarar makamai, da rura wutar rikici da ka iya haifar da rikice-rikice na zamantakewa da haifar da rashin hadin kai a Najeriya.

Kara karanta wannan

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugabannin Yarbawa, ciki har da sarakuna, suna hada kai don nuna goyon baya ga mai rajin kare hakkin Yarbawan.

Lauya ya bayyana laifuka 3 da gwamnatin Buhari ke tuhumar Sunday Igboho akai

Babban mai ba da shawara ga Sunday Igboho, mai tayar da zaune tsaye kuma dan awaren Yarbawa, Ibrahim Salami, ya bayyana abin da gwamnatin Najeriya ta fada wa takwararta ta Jamhuriyar Benin don ba da sammacin kame da kuma yiwuwar mika Igboho.

Salami ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta zargi Igboho da safarar makamai zuwa Najeriya, SaharaReporters ta ruwaito.

Da yake magana da BBC Yoruba, lauyan ya ce gwamnatin Najeriya ta kuma zargi Igboho da kiran aware da kuma tayar da hankalin kasar.

Legit Hausa ta tattauna da wani lauya, Barista Taofik Yahaya, wanda ya bayyana cewa Najeriya zata samu dawo da Igboho gida saboda kwarjinin da take da shi wajen kasashen da makwabtaka da Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi hukunci kan Sunday Igboho, ta kuma saki matarsa

Ya kara da cewa abubuwan da Igboho yayi barazana ne ga cigaban zaman Najeriya kasa guda.

Yace:

"Idan Najeriya na da alaka mai kyau da kasar da yake yanzu, za'a iya fara shirin dawo da shi. Gwamnatin tarayya zata rubutawa gwamnatin Benin wasika bukatar hakan."

Kotu ta yi hukunci kan Sunday Igboho, ta kuma saki matarsa

A wani labarin, wata kotu mai suna Cour De’appal De Cotonou, Jamhuriyar Benin, inda aka gurfanar da dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo (Igboho) da matarsa a ranar Alhamis, ya ba da umarnin a saki matar da yammacin yau.

SaharaReporters ta samu labarin daga jami’an kotun cewa kotun ta yanke hukuncin cewa a mayar da Igboho zuwa gidan yari.

Wani jami'i ya ce:

“Sun gama zaman kotu. Matar za a sake ta a daren yau kuma Sunday zai ci gaba da kasancewa a tsare. An dage batun har zuwa ranar Juma’a.”

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'an Jamhuriyar Benin na yi wa Sunday Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel