FBI: A karshe Abba Kyari ya bayyana a gaban kwamitin bincike na 'yan sanda, ya kare kansa daga tuhuma
- Mataimakin kwamishinan 'yan sanda (DCP) da aka dakatar, Abba Kyari, ya bayyana gaban kwamitin bincike na musamman (SIP) kan zargin alakarsa da Hushpuppi
- Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta dakatar da Kyari a ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta bayan shawarar IGP Usman Baba
- A ranar Litinin 2 ga watan Agusta ne IGP ya nada DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban rundunar Leken Asiri (IRT)
FCT, Abuja - Bayan dakatarwar da hukumar ‘yan sanda (PSC) ta yi masa, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP) Abba Kyari ya gurfana a gaban kwamitin bincike na musamman kan tuhumarsa a badakalar Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa har zuwa lokacin da aka dakatar da shi, Kyari shine shugaban dakarun IRT masu tattara bayanan sirri, kuma kwamitin da ke binciken sa yana karkashin Joseph Egbunike, mataimakin babban sufeton yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar.
Legit.ng ta tattaro cewa jaridar ta lura cewa Kyari ya kare kansa a gaban SIP a hedkwatar rundunar, Abuja, a ranar Talata, 3 ga watan Agusta, ya kara da cewa SIP ya kammala zaman da misalin karfe 8 na dare.
Majiyar ta ce:
“Kwamitin ya fara zama tun ranar Litinin. Kyari ya bayyana a gaban membobin kwamitin a yau (Talata) inda ya kare kansa daga tuhumar da FBI ya yi masa a gaban membobin SIP. Kwamitin zai dauka daga nan.”
Jaridar ta kuma ruwaito cewa Kyari ya musanta aikata ba daidai ba
An yi waje da Abba Kyari, an nada wani a madadinsa
A makon jiya aka dakatar da DCP Abba Kyari daga bakin aiki, DCP Tunji Disu ne ya gaje shi a matsayin shugaban dakarun IRT masu tattara bayanan sirrri.
IGP ya ce Disu zai rike Rundunar IRT yayin da ake binciken zargin da ake yi wa Kyari. Usman Alkali Baba Disu zai shiga ofis ba tare da wani bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng