Karin Bayani: DSS Ta Bi Umarnin Kotu, Ta Gabatar da Dukkan Hadiman Sunday Igboho a Kotu
- Hukumar DSS ta gabatar da gaba ɗaya hadiman Sunday Igboho 12 dake tsare a hannunta gaban kotu
- Wannan ya biyo bayan umarnin da kotun ta baiwa DSS a zamanta da ya gabata
- DSS ta kame makusanta Igboho ne yayin wani farmaki da takai gidansa kwanakin baya
Abuja:- Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gabatar da gaba ɗaya hadiman Sunday Igboho a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja ranar Laraba, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Wannan yazo ne kasa da awanni 72 bayan kotu ta baiwa hukumar umarnin ta gabatar da baki ɗaya makusantan jagoran yan awaren kafa kasar yarbawa.
A zaman kotun na ranar Litinin, DSS ta gabatar da mutum takwas ne kacal a gaban kotun.
An kame mutanen ne a ranar 1 ga watan Yuli, yayin da jami'an DSS suka kai hari gidan Sunday Igboho, kamar yadda punch ta ruwaito.
Amma lauyan dake kare su, Pelumi Olajengbesi, ya shigar da kara gaban kotu cewa an tauye musu hakkinsu na yan adam.
Me ake zarginsu da shi?
Jami'an DSS sun kame hadiman Igboho ne suna zarginsu da tara makamai domin ta da rikici a kasa.
Igboho ya jawo hankalin mutane da dama a kafafen sada zumunta yayin da ya baiwa fulanin Ibarapa wa'adi su bar yankin baki ɗaya bayan kashe Dr. Aborode.
Igboho ya musanta zargin da ake masa
A ranar 28 ga watan Yuli, Sunday Igboho ya musanta zargin da gwamnatin tarayya take masa cewa yana shigo da makamai domin tada hargitsi a ƙasa.
Shugaban lauyoyinsa, Ibrahim Salami, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata bayan zaman kotu a ƙasar Benin.
Salami yace:
"Igboho ya faɗawa kotu cewa ba shi da laifin komai a Najeriya, ya shaidawa alakali cewa gwamnatin Najeriya ta sanya shi cikin waɗanda take nema ne sabida yana kare yarbawa daga ta'addancin fulani makiyaya."
"Yace ya tsere daga Najeriya ne saboda gwamnati na neman hallaka shi."
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kutsa Wurin Ibada Sun Hallaka Babban Malami Yana Tsaka da Addu'a
Wasu yan bindiga sun kutsa wurin ibadar kirista (Cocin RCCG) sun harbe Fasto Bolanle Ibrahim, har lahira a jihar Lagos.
Yan bindigan sun yi kokarin tafiya da Fasto Ibrahim, amma wani babban fasto na gaba da shi ya dakatar da su da tambayar me suke bukata.
Asali: Legit.ng