A karshe tsohon Shugaban INEC ya yi watsi da APC da PDP, ya shiga PRP, ya bayyana dalilai

A karshe tsohon Shugaban INEC ya yi watsi da APC da PDP, ya shiga PRP, ya bayyana dalilai

  • Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ya koma jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP)
  • Wa'adin Jega a matsayin shugaban INEC ya ƙare a ranar 30 ga Yuni, yan watanni bayan ya gudanar da zaɓen 2015
  • A cewarsa, duka jam’iyyun APC da PDP mai mulki sun gazawa yan Najeriya

Kaduna, Kaduna - Shekaru shida bayan karewar wa'adin mulkinsa a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya sanar da matakinsa na yin siyasar bangaranci gabanin babban zaben 2023.

The News ta rahoto cewa Jega ya koma jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) sabanin hasashen da wasu bangarorin suka yi na cewa farfesa na iya hadewa da jam'iyyar All Progress Congress (APC) mai mulki.

A karshe tsohon Shugaban INEC ya yi watsi da APC da PDP, ya shiga PRP, ya bayyana dalilai
Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega ya koma jam,'iyyar PRP Hoto: Attahiru Jega

Legit.ng ta tattaro cewa yayin bayar da dalilinsa na zabar PRP, ya ce saboda manyan jam’iyyun biyu - All progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) ba su cika muradin ‘yan Najeriya ba.

Kara karanta wannan

PDP ba sa'ar APC bace: PDP ta yi martani kan Jega bisa kwatanta ta da APC

Jega ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su watsar da jam’iyyun biyu saboda mugayen halayensu a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Jaridar ThisDay ta kuma ruwaito cewa Jega ya bayyana zama memba na sabuwar jam'iyyar siyasa, PRP kuma ya shawarci 'yan Najeriya da kada su zabi APC da PDP a zaben 2023.

Sai dai, ya lura cewa karuwar amfani da fasaha shine mafi kyawun aiki a duniya don inganta amincin zaɓe.

Duk lalacewa mun fi PDP: APC ta caccaki Attahiru Jega bisa kwatanta ta da PDP

A gefe guda, jam'iyyar APC ta mayar da martani kan maganganun baya-bayan nan da aka danganta ga tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega.

Jega ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su zabi jam’iyya mai mulki APC da jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023.

Wata sanarwa da mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya aikewa Legit.ng a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki bata ji dadin kwatanta ta da PDP ba.

Kara karanta wannan

Duk lalacewa mun fi PDP: APC ta caccaki Attahiru Jega bisa kwatanta ta da PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel