Duk lalacewa mun fi PDP: APC ta caccaki Attahiru Jega bisa kwatanta ta da PDP
- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, bata ji dadin yadda Jega ya kwatanta ta da jam'iyyar PDP ba
- A cewar APC, wannan mummunan kwatance ne wanda yake ba daidai ba kuma ba gaskiya ba
- Ta ce a halin yanzu, tana kokarin gyara kura-kuran PDP ne na tsawon shekaru 16 da suka gabata
Abuja - Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan maganganun baya-bayan nan da aka danganta ga tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega.
Jega ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su zabi jam’iyya mai mulki APC da jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023.
Wata sanarwa da mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya aikewa Legit.ng a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki bata ji dadin kwatanta ta da PDP ba.
Sashin sanarwar ya ce:
“An jawo hankalin mu ga rashin kulawa, ba daidai ba, da hargitsi na siyasa wanda tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya yi inda ya yi wa APC, tare da PDP kudin goro.
“Yayin da PDP ta kasa cimma burin 'yan Najeriya a matsayin gwamnati da kuma jam’iyyar adawa, APC na ci gaba, na cikin koshin lafiya kuma tana tsaftace babban barnar da PDP ta bari wanda ta kasa samar da romon dimokuradiyya ga al’ummar Najeriya bayan shekaru 16. .
“Yayin da Farfesa Jega ya fadi gaskiya game da PDP, jam’iyyar da a karkashinta ya kasance shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa, mun ki amincewa da kwatanta APC da PDP.
"Farfesa Jega ya yi kuskure game da batunsa kuma ya cakuda su a kwatancensa na PDP da APC."
Jam'iyyar APC ta soki Jega kan watsi da karatunsa, inda ya kara da cewa ya shiga fagen siyasar PDP.
Jam'iyyar mai mulki ta kuma bayyana cewa Jega na kokarin kaddamar da harkokin siyasa a cikin wata jam'iyyar siyasa.
APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu
Tshon shugaban hukumar INEC, farfesa Attahiru jega ya gargadi 'yan Najeriya kan sake zaban shugabanni daga jam'iyyun APC da PDP.
A cewarsa, wadannan jam'iyya dukkansu hali daya suke tafe akai, kuma babu abinda suka taba wa 'yan Najeriya tsawon shekaru 20 da suka yi suna mulki.
Jega ya bayyana haka ne yayin wata hira da sashin Hausa na BBC, wanda Legit Hausa ta tattaro yana cewa, babu bukatar sake yin imani da jam'iyyun a nan gaba kasancewar sun gagara cimma wani abin kirki tsawon shekaru.
A yanzu kam manufar mu ita ce sama wa 'yan Najeriya aiki, in ji Gwamnatin Buhari
A wani labarin, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fifita samar da ayyukan yi a kasar cikin shekara guda.
Osinbajo, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Laolu Akande, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da yada labarai, ya aikewa Legit.ng.
Ya ce gwamnatin tarayya ta fifita bukatar samar da ayyukan yi a dukkan manyan manufofinta, ayyukanta da shirye-shiryenta.
Asali: Legit.ng