PDP ba sa'ar APC bace: PDP ta yi martani kan Jega bisa kwatanta ta da APC

PDP ba sa'ar APC bace: PDP ta yi martani kan Jega bisa kwatanta ta da APC

  • Jam'iyyar PDP ita ma ta fusata bisa kwatanta ta da APC da farfesa Attahiru Jega ya yi
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa, Jega bai yi daidai ba wajen gama nasarorin PDP da na APC
  • PDP ta bayyana wasu manyan nasarori da ta cimma yayin da APC kuwa ta ke rusa kasa

Abuja - Jam'iyyar PDP ta ce, ba daidai bane wani ya tsaya yana kwatanta nasarorinta da na jam'iyyar APC mai mulki a yanzu ba, jaridar Sun ta ruwaito.

Wannan na fito wa ne daga bakin kakakin ta na kasa, Kola Ologbondiyan a jiya Litinin 2 ga watan Agusta yayin da ya yake martani ga kalaman tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Legit.ng ta tattaro cewa Ologbondiyan ya ce yayin da PDP a cikin shekaru 16 na mulkinta ta biya bashin kasar tare da sake farfado da tattalin arziki gami da manyan ayyuka da aka samar ga 'yan kasa, APC ta lalata tattalin arzikin kasar ne.

PDP ba sa'ar APC bace: PDP Ta yi martani kan jega bisa kwatanta ta da APC
APC da PDP | Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Duk lalacewa mun fi PDP: APC ta caccaki Attahiru Jega bisa kwatanta ta da PDP

A bangare guda, jam'iyyar APC ta mayar da martani kan maganganun baya-bayan nan da aka danganta ga tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega.

Jega ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su zabi jam’iyya mai mulki APC da jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023.

Wata sanarwa da mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya aikewa Legit.ng a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki bata ji dadin kwatanta ta da PDP ba.

Sashin sanarwar ya ce:

“An jawo hankalin mu ga rashin kulawa, ba daidai ba, da hargitsi na siyasa wanda tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya yi inda ya yi wa APC, tare da PDP kudin goro.
“Yayin da PDP ta kasa cimma burin 'yan Najeriya a matsayin gwamnati da kuma jam’iyyar adawa, APC na ci gaba, na cikin koshin lafiya kuma tana tsaftace babban barnar da PDP ta bari wanda ta kasa samar da romon dimokuradiyya ga al’ummar Najeriya bayan shekaru 16.

“Yayin da Farfesa Jega ya fadi gaskiya game da PDP, jam’iyyar da a karkashinta ya kasance shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa, mun ki amincewa da kwatanta APC da PDP.
"Farfesa Jega ya yi kuskure game da batunsa kuma ya cakuda su a kwatancensa na PDP da APC."

APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu

A tun farko, tshon shugaban hukumar INEC, farfesa Attahiru jega ya gargadi 'yan Najeriya kan sake zaban shugabanni daga jam'iyyun APC da PDP.

A cewarsa, wadannan jam'iyya dukkansu hali daya suke tafe akai, kuma babu abinda suka taba wa 'yan Najeriya tsawon shekaru 20 da suka yi suna mulki.

Jega ya bayyana haka ne yayin wata hira da sashin Hausa na BBC, wanda Legit Hausa ta tattaro yana cewa, babu bukatar sake yin imani da jam'iyyun a nan gaba kasancewar sun gagara cimma wani abin kirki tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel