2023: Fadar Shugaban kasa ta caccaki PDP, ta ce karin gwamnoni za su sauya sheka zuwa APC

2023: Fadar Shugaban kasa ta caccaki PDP, ta ce karin gwamnoni za su sauya sheka zuwa APC

  • Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce wasu gwamnonin PDP na shirin komawa APC
  • PDP ta zargi APC da tilasta wa gwamnoni da mambobinta shiga jam’iyya mai mulki gabanin zaben 2023
  • Sai dai kuma, Adesina ya shawarci shugabannin PDP da su zargi kansu game da halin kunci da jam’iyyar ta shiga a cikin ‘yan watannin da suka gabata

Aso Rock, Abuja - Fadar shugaban kasar Najeriya ta mayar wa PDP da martani kan ikirarin da ta yi na cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta mayar da fadar Villa hedkwatarta.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa gwamnonin PDP sun yi wani taro a Bauchi a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, sun zargi APC da tilasta wa ‘yan PDP da sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

2023: Fadar Shugaban kasa ta caccaki PDP, ta ce karin gwamnoni za su sauya sheka zuwa APC
Fadar Shugaban kasa ta ce karin gwamnoni za su sauya sheka zuwa APC Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya caccaki gwamnonin kan murkususu da suke yi sakamakon masifar da jam'iyyar su ta tsinci kanta a ciki.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP masu rashawa ne ke komawa APC, In ji Gwamna Tambuwal

Da yake magana daga Ingila (UK) a wata hirar talabijin, Adesina ya yi ikirarin cewa wasu daga cikinsu (gwamnonin PDP) sun zo Villa da daddare ba tare da sanarwa ba.

Gwamnonin PDP na cikin tattaunawar sauya sheka da shugabannin APC

Ya ce wasu gwamnonin PDP suna tattaunawa da shugabannin APC kan shirin sauya sheka, yana mai cewa da yawa daga cikinsu za su bar jam’iyyarsu a shekara mai zuwa lokacin da Shugaba Buhari zai fara kaddamar da ayyuka.

Adesina ya ce:

“Za a gabatar da gagarumin aikin more rayuwa zuwa 2022; farawa daga ƙaddamar da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan wacce PDP ba ta iya cimmawa ba a cikin shekaru 16, zuwa Bututun AKK da manyan tituna da yawa. Wadannan manyan ayyukan za su sa gwamnonin PDP da yawa su shigo APC.”

Ya bayyana PDP a matsayin jam’iyya mai rikitarwa da ke cikin rudani gaba daya, ya kara da cewa daga yanzu zuwa 2023, za a samu karin rudani a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Kuna Yaudarar Kanku Ne, Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Ga Gwamnonin PDP

Adesina ya lura cewa babu wanda ya yi hayaniya a lokacin da su (PDP) ke gudanar da taron BoT (Kwamitin Amintattu) a lokacin mulkin Obasanjo (Olusegun) Yar’Adua (Umaru) da Jonathan (Goodluck).

Yayi mamakin me yasa shugabannin jam'iyyar adawa suke korafi yanzu.

Kan rashin tsaro, ya ce akwai kalubale a wasu fannoni amma hakan ba yana nufin abubuwa masu kyau ba su faruwa a kasar ba.

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

A wani labarin, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

A cewar jaridar Vanguard, Ohakim ya koma APC ne a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, a mahaifarsa dake Okohia a karamar hukumar Isiala Mbano na jihar inda ya karbi tutar jam’iyyar daga shugaban, Marcellenus Nlemigbo.

Tsohon gwamnan ya ce ya yanke shawarar ne domin ra’ayin mutane saboda su ne zabinsa na farko, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba Bu Wanda Zai Tsoratar Da Mu Domin Mu Shiga APC, Gwamnonin PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng