Gwamna Zulum ya zabi mazajen mafarauta 1000 domin kare manoma daga Boko Haram
- Gwamnan jihar Borno ya rantsar da mafarauta 1000 domin yakar 'yan ta'addan Boko Haram
- Gwamnan ya yi haka ne domin kare manoma a wasu sassan garin Maiduguri da sauransu
- Ya kuma yaba wa sojoji da sauran hukumomin tsaro bisa namijin kokarinsu kan wannan aiki
Jihar Borno - Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno, a ranar Alhamis, ya rantsar da mafarauta 1,000 domin yaki da Boko Haram, The Cable ta ruwaito.
Aikin mafarautan shi ne kare manoman da ke noma albarkatun gona a wajen garin Jere, babban birnin Maiduguri, kananan hukumomin Konduga da Mafa na jihar.
An rantsar da mafarautan ne makonni kadan bayan jami'an tsaro na farin kaya (DSS) da sojojin sun gama tantance su.
Gwamnan ya ce:
"Mafarautanmu na cikin gida sun zama wani bangare na labarin nasararmu saboda rawar da suke takawa a kokarin magance matsalolin tsaro da muke fuskanta a jihar.
“Wannan ya sa muka tsunduma neman karin mafarauta don taimaka wa sojojinmu a kokarin da suke yi wanda ba za a iya musantawa ba kuma abin yabo na kokarin kawo karshen tayar da kayar baya.”
A jawabin maraba, dan majalisar Satomi Ahmed, mamba mai wakiltar Jere a majalisar wakilai, ya yaba wa Zulum kan jajircewarsa na tsare rayuka da dukiyoyin mutanen Borno.
Zulum tun a shekarar 2019 ya fara daukar dubban mafarauta da aka zakulo daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya, don shiga jami'an sa kai ta JTF da kuma 'yan banga.
Rantsarwar ta samu halartar Usman Jidda Shuwa, sakataren gwamnatin jihar Borno; Simon Malgwi, shugaban ayyuka, kwamishinoni da sauran jami'an gwamnati.
Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10 a jiya Talata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.
Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.
Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi
A wani labarin, Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba Naira miliyan 21.7 ga gundumomi 87 don sayan shanun sallah ga marayu, Daily Trust ta ruwaito.
An ba kowace daga cikin gundumomin N200,000 na sayen saniya da kuma N20,000 don jigilar ta.
A yayin kaddamar da bayarwar, Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar Said, ya gode wa gwamnatin jihar bisa ci gaba da wannan aikin duk da raguwar albarkatun ta.
Asali: Legit.ng