Yadda wasikar Jakadan Najeriya, Tukur Buratai ta taimaka wajen cafke Igboho a kasar Benin

Yadda wasikar Jakadan Najeriya, Tukur Buratai ta taimaka wajen cafke Igboho a kasar Benin

Tukur Yusuf Buratai ya taimaka wajen cafke Sunday Igboho a garin Cotonou

Sabon Jakadan Najeriyan ya rubuta takarda zuwa ga Gwamnatin kasar wajen

Tsohon shugaban hafsun sojan kasan ya na da alaka mai kyau da DSS da NIA

Tsohon shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya taimaka wajen cafke Sunday Igboho a Benin.

Crime Channels ta ce Tukur Yusuf Buratai ya bada gudumuwa wajen kama wannan mutumi tare da mai dakinsa, Rapo, a hanyarsu ta zuwa kasar Jamus.

An dade da gane gudun ruwan Igboho

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomi da jami’an Najeriya sun dade da gano inda Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya boye.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun yi ram da Sunday Igboho a filin jirgin sama

Jami’an tsaro sun kyale Sunday Igboho ne domin su iya kama shi cikin ruwan sanyi, ba tare da an zubar da jini ba, hakan kuwa aka yi a daren Talatar nan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

A lokacin da Igboho ya samu takardar fasfon bogi, sai gwamnatin tarayya ta kara sa masa ido.

Najeriya ta sanar da kasashen da ta ke makwabtaka da su cewa su yi hattara da Igboho. A ranar Litinin aka kama shi a filin jirgin Cadjèhoun da ke Cotonou.

Takardar Buratai ta hana Igboho zuwa Jamus

Tukur Yusuf Buratai wanda bai dade da zama Jakadan Najeriya a kasar Benin ba, ya rubuta wa gwamnatin kasar Benin takarda a game da wannan mutum.

Jakadan Najeriya, Tukur Buratai
Buratai da Buhari Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Babu ruwan Neja-Delta da maganar kasar Biyafara inji Edwin Clark

Buratai ya na aiki ne tare da jami’an tsaron leken asiri na DSS da na harkokin kasashen waje, NIA.

Wani jami’in tsaro ya sanar da PRNigeria cewa Janar Buratai (mai ritaya), ya dage a kan sai an kama Igboho, kuma an dawo da shi Najeriya daga Cotonou.

Takardar sabon jakadan ya shiga hannun gwamnatin Benin ne ta ofishin jakadancin Najeriya, wannan ya taimaka sosai wajen hana shi zuwa kasar Jamus.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Lauyan Sunday Igboho, Yomi Alliyu SAN ya ce Igboho da mai dakinsa, su na kokarin hawa jirgin sama zuwa kasar Jamus ne sai jami'an Interpol suka cafke su.

Alliyu ya ce bai kamata a dawo da Igboho gida ba,kamar yadda yarjejeniyar dake tsakanin gwamnatin Najeriya da sauran kasashen Afirka ta tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng