Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus

Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus

  • Lauyan Sunday Igboho, Yomi Alliyu, ya yi kira ga kasashen duniya game da kame wanda yake karewa
  • Alliyu ya ce bai kamata a dawo da Igboho ba kamar yadda yarjejeniyar dake tsakanin Najeriya da wasu kasashen Afirka makwabta ta tanada
  • Lauyan wanda ya fitar da sanarwa a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, ya dage cewa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka ba daidai bane

An bayyana cikakkun bayanai game da yadda jami'an tsaro suka kama dan awaren Yarbawa Sunday Adeyemo (wanda aka fi sani da Igboho) ga duniya baki daya.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, Lauyan Igboho, Yomi Alliyu (SAN) ya bayyana cewa wanda yake karewa na kokarin hawa jirgin zuwa kasar Jamus tare da matarsa Bajamushiya lokacin da jami'an 'yan sanda na Interpol suka bi su tare da kwamushe su.

Alliyu ya ce an danke shi ne a Jamhuriyar Benin, wata kasar Afirka mai makwabtaka da Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus
Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Lauyan ya yi nuni da kamun na Igboho a matsayin abin takaici da rashin adalci, ya kara da cewa ya kamata gwamnatin Jamus tare da kasashen duniya su tashi tsaye kan wannan lamari.

Sanarwar a wani bangare ta ce:

"... ku tashi tsaye don hana zartar da hukuncin Gwamnatin Najeriya ta hanyar kin amincewa da duk wata bukata ta neman tasa keyar wanda muke karewa wanda tuni ya gabatar da bukatar a gaban Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa."

Ya yi ikirarin cewa bisa yarjejeniyar dawo da mutum ta 1984, tsakanin Najeriya, Togo Benin da Ghana, an cire mutane irin su Igboho a ciki.

Jaridar The Nation ta kawo karin bayanin:

“Yarjejeniyar dawo da mutane na 1984 tsakanin Togo, Najeriya, Ghana da Jamhuriyar Benin an cire wadanda suka gudu saboda siyasa."

Kara karanta wannan

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Labari mai zafi: Jami’an tsaron kasar waje sun yi ram da Sunday Igboho zai tsere zuwa Jamus

Rahotanni suna bayyana cewa hukumoni sun kama Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an cafke Mista Sunday Adeyemo a birnin Cotonou, kasar Nijar. An kama Igboho ne ya na shirin ruga wa zuwa kasar Jamus.

Rahoton ya bayyana cewa hukumomin kasashen kasar Afrika ta yamman sun tsare Igboho, ana kuma sa ran shigo wa da shi Najeriya nan ba da dade wa ba.

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan hukuncin harbe 'yan bindiga a Najeriya

A wani labarin, tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce harsasai da sauran karfin makamai su kadai ba za su iya dakatar da fashi da makami, bindiganci da sauran nau'ikan aikata laifuka a kasar ba.

Kara karanta wannan

Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47

Ya fadi haka ne a ranar Lahadi a Abuja yayin bikin cikar shekaru 50 na tsohon Corps Marshal na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Osita Chidoka.

A cewarsa, magance ta'addanci da aikata laifuka yana bukatar manyan shirye-shirye masu inganci na gwamnati, fasaha da sauran dabaru, Reuben Abati ya tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.