Labari mai zafi: Jami’an tsaron kasar waje sun yi ram da Sunday Igboho zai tsere zuwa Jamus

Labari mai zafi: Jami’an tsaron kasar waje sun yi ram da Sunday Igboho zai tsere zuwa Jamus

Hukumomi sun kama Sunday Adeyemo a kasar Benin ranar Litinin cikin dare

Wannan mutum da aka fi sani da ‘Igboho’ ya na shirin tserewa ne zuwa Jamus

Bisa dukkan alamu a yau za a dawo da Sunday Igboho Najeriya daga Cotonou

Rahotanni suna bayyana cewa hukumoni sun kama Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa a Najeriya.

An damke Sunday Adeyemo a kasar Benin

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an cafke Mista Sunday Adeyemo a birnin Cotonou, kasar Nijar. An kama Igboho ne ya na shirin ruga wa zuwa kasar Jamus.

Rahoton ya bayyana cewa hukumomin kasashen kasar Afrika ta yamman sun tsare Igboho, ana kuma sa ran shigo wa da shi Najeriya nan ba da dade wa ba.

KU KARANTA: Igboho ya lashe aman da ya yi kan shirya gangami

Yunkurin tuntubar mai magana da yawun bakin hukumar DSS, Peter Afunanya da ‘yan jarida su ka yi bai yiwu ba, jami’in bai amsa sakonni da kiran waya ba.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Punch ta ce an kama wannan mutumi ne a ranar Litinin da daddare, kamar yadda wani wanda ya samu labarin abin da ya wakana ya shaida manema labaran.

An shafe kusan kwanaki 20 ana neman Sunday Adeyemo

Jami’an tsaro sun kama Igboho ne bayan makonni uku da DSS ta soma cigiyarsa a Najeriya da laifuffukan da su ka hada da ajiye makamai a cikin gidansa.

“An kama shi a ranar Litinin cikin dare a Jamhuriyyar Benin. Ya a shirin zuwa kasar Jamus ne. Jami’an tsaron Benin za su dawo da shi Najeriya ranar Talata.”
Sunday Igboho
Sunday Igboho
Asali: Facebook

KU KARANTA: An samu bindiga, layu, da guraye a gidan Igboho

Ana sa ran dawo da Sunday Adeyemo mai shekaru 48 daga kasar Benin mai kusanci da Najeriya a bangaren yammacin nahiyar Afrika ba zai yi wani wahala ba.

Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto, an shiga gidan wannan mutumi ne a ranar 1 ga watan Yuli, 2021, amma ba a same shi ba, aka kama wasu mutum 13.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

Tun wancan lokaci, hukumar DSS ta yi alkawarin cewa za a damko Igboho a duk inda ya shiga.

Idan mu ka koma siyasar yankin, za mu ji tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu ne ya hana Tunde Bakare zama abokin takarar Muhammadu Buhari a zaben 2015.

Nasir El-Rufai ya so Fasto Bakare ya zama Mataimakin Shugaban kasa, amma Tinubu ya kawo Yemi Osinbajo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel