Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa
- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyarsa ta zakulo masu aikata laifuka a Najeriya
- Ya bayyana haka ne bayan kame shugaban 'yan awaren Yarbawa, Sunday Igboho a garin Cotonou
- A baya shugaban ya ce dama zai ji da duk masu aikata laifuka a kasar da yaren da suke fahimta
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a kara himma don zakulo wadanda ke dagula zaman lafiyar kasar da barazana ga 'yan kasar.
Ya bayar da wannan tabbacin ne 'yan sa'o'i bayan da aka kama wani dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho.
Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa da Kasa (Interpol) ta kame Igboho a Cotonou, Jamhuriyar Benin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Buhari, duk da bai yi magana kai tsaye ba game da kamun Igboho, ya ba da tabbacin zakulwar ne a garinsa na Daura ta Jihar Katsina, bayan Sallar Idin Layya.
KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam
Shugaban ya yi barazanar tunkarar masu laifi da masu neman ballewa “Da yaren da suke fahimta”.
An kama Shugaban kungiyar ta 'yan aware ta IPOB 'yan kwanaki bayan sanarwar da kakakin shugaban kasar ya fitar.
A cikin wata sanarwa da hadiminsa na yada labarai, Garba Shehu ya fitar, an ruwaito Buhari yana umartar jami'an tsaro da su zama masu jajircewa wajen wanzar da zaman lafiya a kasar.
Hakazalika an bukacesu da su tabbatar da kyakkyawar dangantaka da al'ummomi ta yadda za su iya karbar bayanan sirri.
Kalaman na Buhari sun zo ne yayin da gwamnatin tarayya ta fara yunkurin kammala aikin dawo da Igboho wanda aka kame tare da matarsa Bajamushiya, Ropo, a kan hanyarsu ta zuwa Jamus.
Labari mai zafi: Jami’an tsaron kasar waje sun yi ram da Sunday Igboho zai tsere zuwa Jamus
Rahotanni suna bayyana cewa hukumoni sun kama Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an cafke Mista Sunday Adeyemo a birnin Cotonou, kasar Nijar. An kama Igboho ne ya na shirin ruga wa zuwa kasar Jamus.
Rahoton ya bayyana cewa hukumomin kasashen kasar Afrika ta yamman sun tsare Igboho, ana kuma sa ran shigo wa da shi Najeriya nan ba da dade wa ba.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara
Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus
A wani labarin, An bayyana cikakkun bayanai game da yadda jami'an tsaro suka kama dan awaren Yarbawa Sunday Adeyemo (wanda aka fi sani da Igboho) ga duniya baki daya.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, Lauyan Igboho, Yomi Alliyu (SAN) ya bayyana cewa wanda yake karewa na kokarin hawa jirgin zuwa kasar Jamus tare da matarsa Bajamushiya lokacin da jami'an 'yan sanda na Interpol suka bi su tare da kwamushe su.
Alliyu ya ce an danke shi ne a Jamhuriyar Benin, wata kasar Afirka mai makwabtaka da Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng