Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

  • Rahotanni daga jihar Oyo asun bayyana yadda 'yan sanda asuka fatattaki masu zanga-zanga a Ibadan
  • An ce sun fito zanga-zanga ne domin nuna adawa da kame Sunday Igboho dan awaren Yarbawa
  • An kame Sunday Igboho ne a Cotonou ta jamhuriyar Benin, inda har yanzu gwamnatin Najeriya bata ce komai akai ba

‘Yan sanda dauke da makamai sun tarwatsa magoya bayan Sunday Igboho da ke gudanar da zanga-zanga a Ibadan don nuna adawa da kamun dan awaren na Yarbawa.

An cafke Igboho ne tare da Matarsa Ropo a daren Litinin a Cotonou, Jamhuriyar Benin a kan hanyarsa ta zuwa Jamus.

Su biyun a yanzu haka suna tsare a Jamhuriyar Benin. Sai dai, Gwamnatin Tarayya ba ta ce komai game da kama Igboho da tsare shi a cikin kasar ta waje ba.

KARANTA WANNAN: Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Neman Kafa Kasar Yarbawa Za Su Yi Zanga-Zanga Kan Tsare Igboho a Kotonou

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho yayin zanga-zanga
Rundunar 'yan sanda ta Najeriya | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: Facebook

An ce masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa tashar motar bas ta Soka a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, inda suka rera wasu wakoki tare da neman a saki Igboho.

Mazauna yankin sun ce masu zanga-zangar, wadanda ke dauke da alluna dauke da rubutu daban-daban, sun hada da maza da mata.

An ce sun yi kira ga shugabannin Yarbawa da na sauran kasashen duniya su yi gwagwarmaya don a sako Igboho.

Daya daga cikin ’yan kasuwar kan titi a tashar ta Soka ya shaida wa manema labarai cewa magoya bayan Igboho sun yi cincirindo, suna gargadin Gwamnatin Tarayya da kar ta kashe Igboho kamar yadda aka kashe kashe MKO Abiola.

Ya kuma ce zanga-zangar ta dakatar da zirga-zirga a yankin lamarin da ya kai ga wasu masu ababen hawa da ke kan hanya dole su bi wasu hanyoyi don kaucewa hargitsi.

Wani mazaunin yankin wanda ya bayyana kansa a matsayin Musbau Ogunbiyi ya ce zanga-zangar ta fara ne da misalin karfe 1.50 na yamma.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Ya ce:

"'Yan sanda sun shigo kimanin motocin sintiri hudu da wata mota. Sun yi harbin iska sun kori masu zanga-zangar.”

Amma wani mazaunin yankin, Taye Adeoti, ya ce masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa Unguwar Challenge bayan sun kwashe wasu mintuna a tashar motar.

Wakilin jaridar Punch da ya ga faruwar lamarin ya lura cewa ’yan sanda dauke da makamai sun mamaye wurin da misalin karfe 3:30 na yamma.

'Yan sanda sun tsaya a wurare masu mahimmanci a wurin. Bayan sun daidaita zirga-zirgar ababen hawa, sun dan jima kafin daga bisani su tafi.

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a kara himma don zakulo wadanda ke dagula zaman lafiyar kasar da barazana ga 'yan kasar.

Ya bayar da wannan tabbacin ne 'yan sa'o'i bayan da aka kama wani dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho. Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa da Kasa (Interpol) ta kame Igboho a Cotonou, Jamhuriyar Benin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus

Buhari, duk da bai yi magana kai tsaye ba game da kamun Igboho, ya ba da tabbacin zakulwar ne a garinsa na Daura ta Jihar Katsina, bayan Sallar Idin Layya.

KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus

A wani labarin, An bayyana cikakkun bayanai game da yadda jami'an tsaro suka kama dan awaren Yarbawa Sunday Adeyemo (wanda aka fi sani da Igboho) ga duniya baki daya.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, Lauyan Igboho, Yomi Alliyu (SAN) ya bayyana cewa wanda yake karewa na kokarin hawa jirgin zuwa kasar Jamus tare da matarsa Bajamushiya lokacin da jami'an 'yan sanda na Interpol suka bi su tare da kwamushe su.

Alliyu ya ce an danke shi ne a Jamhuriyar Benin, wata kasar Afirka mai makwabtaka da Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Jami’an tsaron kasar waje sun yi ram da Sunday Igboho zai tsere zuwa Jamus

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel