Yanzu-Yanzu: Hoton Yadda Aka Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe

Yanzu-Yanzu: Hoton Yadda Aka Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe

  • An yi jana'izar marigayi Manjo Janar Hassan Ahmed da yan bindiga suka kashe a hanyar Okene zuwa Abuja
  • Babban sojan na Nigeria yana cikin motarsa ne tare da matarsa a lokacin da yan bindigan suka kai masa hari a daren ranar Alhamis
  • Rundunar sojojin Nigeria ta tabbatar da rasuwarsa tare da aike tawaga domin yi wa iyalansa jaje

An birne Hassan Ahmed, Manjo Janar a Rundunar Sojojin Nigeria, wanda yan bindiga suka kashe a daren ranar Alhamis, a makabartar barikin Lungi da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Ahmed, wanda aka nada shi direkta a hedkwatar sojoji ya gamu da ajalinsa ne yayin da yan bindiga suka harbe shi a kusa da Abaji a babban birnin tarayya Abuja.

Wani dan uwan marigayin ya bayyana cewa yan bindigan sun tafi da matarsa bayan halaka shi.

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Harbe Janar Ɗin Sojan Nigeria Har Lahira, Sun Sace Matarsa

Ahmed da matarsa suna dawowa daga Okene a jihar Kogi ne a lokacin da suka gamu da yan bindigan.

Yanzu-Yanzu: An Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe
An Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Rundunar Sojojin Nigeria ta tabbatar da rasuwar Manjo Janar Ahmed

Kakakin rundunar sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da rasuwar Ahmed.

Ya ce babban hafsan sojojin kasa, Laftanat Janar Faruk Yahaya, ya aike da tawaga domin yi wa iyalan mammacin ta'aziyya.

Nwachukwu kuma ce kungiyar matan jami'an sojojin Nigeria, NAOWA, karkashin jagorancin mataimakiyar shugaban kungiyar na kasa, Mrs Stella Omozaje, suma sun ziyarci iyalan domin yi musu ta'aziya.

KU KARANTA: 'Karfin Hali: Ƴan Bindiga Sun Fara Rubutawa Mutane Wasika Kafin Su Kawo Hari a Sokoto

Sanarwar ta ce:

"Cikin tsananin jimami, babban hafsan sojojin kasa Lt Janar Farouk Yahaya, Dakaru da sojojin Nigeria na sanar da rasuwar Manjo-Janar Hassan Ahmed, tsohon Provost Marshall na Rundunar Sojojin Nigeria.
"Abin bakin cikin ya faru ne a yayin da yan bindiga suka kai wa motar babban sojan hari a hanyar Lokoja zuwa Abuja a jiya 15 ga watan Yulin 2021.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta karyata sakin 'yan Boko Haram, ta fayyace gaskiya

"Tawaga daga Hedkwatar sojoji karkashin Shugaban sashin tsare-tsare na Sojoji, Manjo Janar Anthony Omozaje sun ziyarci iyalansa.
"Mambobin kungiyar matan jami'an sojojin Nigeria, NAOWA, karkashin jagorancin mataimakiyar shugaban kungiyar na kasa, Mrs Stella Omozaje, suma sun ziyarci iyalan don yi musu ta'aziya."

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labarin daban, yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel