Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

  • Mr Nnamdi Kanu, shugaban IPOB ya roki kotu ta tura shi gidan yarin Kuje a Abuja
  • Kanu ya yi wannan rokon ne ta bakin lauyansa Ifeanyi Ejiofor yana mai cewa yana shan azaba
  • Shugaban kungiyar na IPOB ya koka kan cewa ajiye cikin kadaici da DSS ta yi yana tamkar azabtarwa ce

Shugaban haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari
Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A bukatar da ya gabatarwa kotu, Ifeanyi Ejiofor, lauyan Kanu ya ce ana galazawa wanda ya ke karewa azaba ta kwakwalwa da wasa da hankali a hannun DSS, The Cable ta ruwaito.

Ya ce saboda adalci a mayar da Kanu hannun hukumar kula da gidajen gyaran tarbiyya na Nigeria.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

Ya ce:

"Likitocin da suke duba wanda ya karewa a tsare a hannun DSS ba su wadata ba, duba da irin halin da ya ke ciki."
"Wanda aka yi karar ya bukatar kwararrun likitoci duba da cewa takardunsa ba babban likitan zuciya na asibitin Nairobi Kenya, wand ake rike da takaurdunsa na asibiti kafin a kama shi sun nuna lafiyarsa na tabarbarewa. An saka kofin takardun domin kotu ta gani."
"Idan ba a bari ya ga likitocin da suka dace ba cikin gaggawa, wanda aka yi karar yana iya mutuwa a tsare tun kafin a yi masa shari'a."

Kara karanta wannan

'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun Ƙwayoyi

"Tunda aka shigo da shi kasar a ranar 27 ga watan Yunin 2021, an tsare shi a daki shi kadai, lauyansa kadai ke iya ganinsa shima sai da izinin shugaban DSS kuma ba koda yaushe ya ke bada izinin ba.
"Wadanda suke tsare da shi suna gallaza masa azaba ta hanyar tsare shi cikin kadaici."

El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya yi matuƙar murnar kama Nnamdi Kanu

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana farin cikinsa game da kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), News Wire ta ruwaito.

Ministan shari'a kuma Attoni Janar na kasa, Abubakar Malami (SAN), a ranar Talata, ya sanar yayin taron manema labarai cewa an kama Kanu tun a ranar Lahadi.

Da ya ke tsokaci a kan kamen lokacin da aka yi hira da shi a BBC Pidgin a ranar Juma'a, El-Rufai ya ce ya yi murna da kama Kanu saboda ya tsere bayan bashi beli sannan yana kirar Nigeria 'Zoo' wato gidan namun daji.

Kara karanta wannan

Kasar Kamaru ta taya Buhari murna bisa nasarar kame Nnamdi Kanu, ta bayyana dalili

Asali: Legit.ng

Online view pixel