Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Harbe Janar Ɗin Sojan Nigeria Har Lahira, Sun Sace Matarsa

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Harbe Janar Ɗin Sojan Nigeria Har Lahira, Sun Sace Matarsa

  • Wasu Yan bindiga sun bindige Manjo Janar Hassan Ahmed har lahira
  • Lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis a kusa da Abaji a birnin tarayya Abuja
  • Manjo Ahmed da matarsa na hanyarsu na komawa Abuja ne daga Okene

Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun halaka Hassan Ahmed, Manjo Janar a Rudunar Sojojin Nigeria, a birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

An harbe Ahmed, wanda a baya-bayan nan aka nada shi direkta a hedkwatar sojoji, a kusa da Abaji a babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Alhamis.

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Harbe Janar Ɗin Sojan Nigeria Har Lahira, Sun Sace Matarsa
'Yan Bindiga Sun Harbe Janar Ɗin Sojan Nigeria Har Lahira, Sun Sace Matarsa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Maharan, a cewar wani dan uwan marigayin sun kuma yi awon gaba da matarsa.

Ahmed da matarsa suna dawowa daga Okene a jihar Kogi ne a lokacin da suka gamu da yan bindigan.

Kara karanta wannan

Fashola: Ba mu da matsalar ƙaranci gidaje a Nigeria, akwai gidaje masu yawa da babu mutane a ciki

Rundunar Sojojin Nigeria ta tabbatar da rasuwar Manjo Janar Ahmed

Kakakin rundunar sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da rasuwar Ahmed.

Ya ce babban hafsan sojojin kasa, Laftanat Janar Faruk Yahaya, ya aike da tawaga domin yi wa iyalan mammacin ta'aziyya.

KU KARANTA: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Nwachukwu kuma ce kungiyar matan jami'an sojojin Nigeria, NAOWA, karkashin jagorancin mataimakiyar shugaban kungiyar na kasa, Mrs Stella Omozaje, suma sun ziyarci iyalan domin yi musu ta'aziya.

Sanarwar ta ce:

"Cikin tsananin jimami, babban hafsan sojojin kasa Lt Janar Farouk Yahaya, Dakaru da sojojin Nigeria na sanar da rasuwar Manjo-Janar Hassan Ahmed, tsohon Provost Marshall na Rundunar Sojojin Nigeria.
"Abin bakin cikin ya faru ne a yayin da yan bindiga suka kai wa motar babban sojan hari a hanyar Lokoja zuwa Abuja a jiya 15 ga watan Yulin 2021.

Kara karanta wannan

Hukumar Sojoji ta saki yan ta'addan Boko Haram 1009, ta mikasu ga gwamnatin Borno

"Tawaga daga Hedkwatar sojoji karkashin Shugaban sashin tsare-tsare na Sojoji, Manjo Janar Anthony Omozaje sun ziyarci iyalansa.
"Mambobin kungiyar matan jami'an sojojin Nigeria, NAOWA, karkashin jagorancin mataimakiyar shugaban kungiyar na kasa, Mrs Stella Omozaje, suma sun ziyarci iyalan don yi musu ta'aziya."

Daily Trust ta ruwaito cewa za a birne marigayin babban sojan a makabartar Lungi Barracks, misalin karfe 10 na safiyar ranar Juma'a.

'Yan bindiga sun kashe mutum 19 a Katsina, sun ƙona gidaje sun sace dabbobi masu yawa

A wani rahoton, a kalla mutane 19 ne suka mutu sannan wasu dama an neme su an rasa bayan yan bindiga kan babura sun kai hari kauyen Tsauwa a karo na biyu a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina a yammacin ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani majiya daga kauyen ya ce maharan sun afka garin ne misalin karfe 5.45 na yamma.

Kara karanta wannan

Hatsarin motocci ya yi sanadin salwantar rayyuka 9 a Yobe

Yan bindigan sun tarwatsa mazauna kauyen suka rika binsu a kan babura, suka harbe 19 har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164